Jirage Marasa Matuƙa 140 Suka Kai Hari Cikin Dare A Ukraine
Published: 13th, February 2025 GMT
Rundunar sojin saman Ukraine, ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hare-hare cikin dare.
Hare-haren sun fi ƙamari a yankunan Odessa da Kharkiv, a cewar sojojin.
Rundunar sojin saman ta kuma ce ta samu nasarar kare wasu hare-haren daga ciki, yayin da ta tabbatar da kakkaɓo 85 daga cikin jiragen.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Nato ke taro a birnin Brussels, inda ake sa ran batun yaƙin Ukraine ne zai mamaye agjandar taron.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Makiyayan Raƙuma ta Yammacin Afirka a ziyarar girmamawa da suka kai Fadar Gwamnati a Dutse.
Ya ce gwamnatin ta himmatu matuka wajen ganin ta kula da lafiyar al’ummar jihar.
Malam Umar Namadi ya kara da cewa, wannan gwamnati tana da masaniya kan haramtattun ayyukan wasu makiyaya, musamman waɗanda ke shigowa daga ƙasashe makwabta.
Ya bayyana shirin gwamnatin jihar na yin rajistar makiyaya domin sauƙaƙa samunsu
idan buƙatar hakan ta taso.
Namadi ya nuna damuwarsa kan yawan asarar rayuka da raunuka daban-daban da jama’a ke fuskanta sakamakon yawaitar raƙuma da ke tsallaka manyan hanyoyi kowacce rana.
A nasa jawabin, babban sakataren Kungiyar Makiyayan Yammacin Afirka a Najeriya, Abubakar Mustapha Andaza, ya ce sun kai ziyarar ne domin su gabatar da kansu ga gwamnan, tare da neman shawarwarin gwamnatin jihar kan yadda za su gudanar da harkokinsu yadda ya dace.
Usman Muhammad Zaria