Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: ‘Yan Sudan Miliyan 30 Ne Suke Bukatar Agajin Jin Kai
Published: 13th, February 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara
Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula, mutane da dama suna gudun hijira da kuma samun karuwar matsalolin bukatun jin kai.
Tondlana ya nuni da cewa: Akwai matsalolin tsaro a Sudan saboda hau-hau-hawar farashin kayayyakin bukatu saboda rashin zaman lafiya a kasar.
Dangane da yanayin yunwa da aka shelanta a wasu yankunan, ya yi gargadin cewa lamarin na kara ta’azzara saboda fadan da ake fama da shi a yankunan da suka hada da yankunan Darfur da Kordofan da Al-jazira, ya kuma kara da cewa: Ba su samun damar isa ga mutanen da ya kamata su kai musu agajin jin kai da neman inganta rayuwarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labara da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka.
Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.
Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa a cikin tsawon shekara daya da rabi.
Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da karfin kungiyar Hamas.
Jaridar ta kuma ce a daidai lokacin da ake maganar tattaunawa domin musayar fursunoni, HKI tana shirin sake amfani da karfin soja domin sake shimfida ikonta a cikin Gaza baki daya.
Danagne da rawar da Amurka take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa, iyalan fursunoni wadanda suke da takardun zama, ‘yan Isra’ila a lokaci daya kuma Amurkawa, gwamnatin Amurka ba sanar da su cewa, Donald Trump yana cikin shirin bai wa Benjamine Netanyauhu cikakken goyon bayan idan ya zartar da fara kai hare-hare ta kasa akan Gaza. Haka nan kuma an sanar da cewa, ko kadan Trump ba zai yi wa Netanyahu matsin lamba akan dole sai ya koma kan batun musayar fursunoni ba ta ruwan sanyi.