Gwamnatin Zamfara Na Biyan Ma’aikatan Bogi N193.6m Duk Wata
Published: 13th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati.
Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan yara 220 da ke karɓar albashi a matsayin ma’aikatan gwamnati.
Rahoton kwamitin ya tabbatar da cewa an tantance ma’aikata 27,109, yayin da 2,363 suka kasance ma’aikatan bogi, 1,082 sun dace su yin ritaya, 395 na aikin kwantiragi, 261 ba su cikin jerin ma’aikata, 213 suna hutun karatu, 220 ƙanana ne, sannan 67 suna aiki a wasu wurare. Binciken ya kuma gano cewa ma’aikata 75 sun samu aiki ba bisa ƙa’ida ba, kuma dukkansu ƙanana ne a lokacin da aka ɗauke su aiki.
Kwamitin ya bada shawarar dakatar da ma’aikata 207 da ba a tantance ba, waɗanda ake biyansu N16,370,645.90 a kowane wata. Haka nan, an gano ma’aikata 12 a cikin jerin masu albashi amma ba su cikin bayanan ma’aikata, inda suke karɓar N726,594 a kowane wata. Gwamnati ta ce za ta ci gaba da wannan tantancewa don tabbatar da gaskiya da rikon amana, musamman duba da fara biyan mafi ƙarancin albashi daga watan Maris.
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ta kai ziyara ga jami’an NAMA a Filin Jirgin Sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.
A yayin ziyarar, Malam Salihu Abubakar ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar hajjojin da suka gabata, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.
Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri tare da roƙon NAMA ta tabbatar da samar da duk wani kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.
A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabon hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai ƙarin bayani cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin ke aiki ne kawai kafin ƙarfe 5 na yamma.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da ƙudurinsa na ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.
Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.
Rel/Adamu Yusuf