Aminiya:
2025-04-15@13:37:25 GMT

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano

Published: 13th, February 2025 GMT

An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.

Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya.

Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi.

Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin.

Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana:

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Haruna Zago Kwankwaso Rashin lafiya rasuwa Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano

Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas

Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki.

Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa da masu faɗan daban suka yi.

“Wasu sun fito faɗan daba, sun ji wa kansu raunuka a Ƙofar Na’isa, amma ba wanda ya zo wajen ’yan sanda a kai shi asibiti,” a cewar Kiyawa.

Sai dai Kiyawa ya ƙara da cewa jami’ansu sun sake komawa unguwar da daddare, inda suka cafke mutum takwas da raunuka a jikinsu da wuƙaƙe.

Kazalika, ya ce sun tattara sunayen mutane daban-daban da ake zarginsu da faɗace-faɗacen daba kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannu.

Aminiya ta rawaito yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin Ƙofar Na’isa da kuma Ƙofar Ɗan Agundi tun bayan dawowar faɗan daban a yayin bukukuwan sallah ƙarama da aka yi kwanan nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
  • Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran titin Abuja zuwa Kano
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
  • Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
  • An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano