Karin Kudin “Data” A Najeriya Ya Fusata Mutanen Kasar Dake Fama Da Matsananciyar Rayuwa
Published: 13th, February 2025 GMT
Mutanen Najeriya suna bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa.
Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da Giga 15, akan Naira 6,000 bayan da a baya take naira 2,000 ( wato daga dala 1.
33-3.99) da hakan yake nufin cewa an rubanya farashin sau uku.
Shi ma kamfanin Airtel ya kara yawan kudaden cajin nashi da kaso mai yawa.
Wannan Karin da kamfanonin su ka yi, ya bakanta ran masu amfani da su, musamman a wannan lokacin da ake fama da yanayi mai tsanani na tattalin arziki.
Kamfanin MTN ya wallafa sanarwa a shafinsa na X cewa; Karin kudin ya zama wajibi domin gabatar da hidimomi masu nagarta ga kwastomominsa, tare da neman gafara ga abokan hulda.
Wani daga cikin masu tofa albarkacin baki akan Karin na MNT; ya walllafa cewa; Rubanya kudi har sau uku? Lallai karshen duniya ya zo.”
Ana hasashen cewa Karin da aka yi zai shafi kananan ‘yan kasuwa da suke dogaro da hanyoyin sadarwar masu saukin kudi domin tafiyar da harkokinsu.
Ya zuwa yanzu dai kamfanin Globacom, da shi ne kamfani na uku mafi grima a cikin kasar, bai yi Karin kudin ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza
Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata.
A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira.
Daga cikin wadanda suka samu raunuka, sojoji 8,600 ne suka sami raunuka daban-daban na jiki, yayin da wasu 7,500 suka samu matsalolin tabin kwakwalluwa ciki har da firgita, damuwa, tashin hankali, rikirkicewar tunani, kamar yadda jaridar ta nakalto daga sashin kula da dabi’ar ma’aikata da ke karkashin Ma’aikatar yakin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kanun labarai