HausaTv:
2025-04-14@16:32:09 GMT

Hamas: Za A Yi Musayar Fursunoni Kamar Yadda Aka Tsara

Published: 13th, February 2025 GMT

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.

A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da  cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara.

Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar  a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na  kiwon lafiya na gaggawa.

Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga cikin Gaza ba tare da kakkautawa ba.

Wasu daga cikin matsalolin da aka warware sun hada bayar da damar shigar da manyan kayan aiki da motocin buldoza na kwace baraguzai, da makamashi, da kuma  magunguna.

Sanarwar da kungiyar ta Hamas ta wallafa a shafinta na “Telegram” ta ambato masu shiga tsakani da su ne kasashen Masar da Katar suna cewa, za su sa ido domin ganin cewa ana aiki da abubuwan da aka yi yarjejeniyar akansu.

Wannan matakin na kungiyar Hamas, ya zo ne bayan da a kwanaki kadan da su ka gabata ta sanar da dakatar da batun sakin fursunonin har illa masha Allah, saboda yadda HKI take take sharuddan yarjeniyar da aka cimmawa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; Tun cin nasarar juyin musulunci, Iran ta zabi hanyar tattaunawa, saboda ta tabbatar da kyakkyawar niyyarta da kuma aiki da hankali a mu’amalrta da duniya.

Limamin na Tehran Ayatullah Saiddiki ya ce, a yayin tattaunawar da za a yi a tsakanin Iran da Amurka wacce za ta kasance ta hanyar shiga tsakani, Iran za ta ji abinda daya bangaren zai fada, sannan kuma ta bayar da jawabi, domin tabbatarwa da duniya cewa ita daula ce mai aiki da hankali, kuma ba ta tsoron tattaunawa.

Ayatullah Siddiki ya yi ishara da zancen jagoran juyin musulunci akan yadda bangaren da ake tattaunawar ba ya aiki da abubuwan da aka cimmawa da amincewa da su.

Haka nan kuma limamin na Tehran ya ambato jagoran juyin musuluncin na Iran yana bayyana yadda Amurka take kiyayya da Jamhuriyar da musulunci na Iran da addinin musulunci da kuma alkur’ani mai girma, saboda asarar manufofinta da ta yi a cikin Iran.

Ayatullah Siddiki ya kuma amabci cewa maganar da shugaban kasar Amurka yake yi na tattaunawa kai tsaye da Iran ba koma ba ne, sai yaudara da ba ta da tushe. Kuma saboda yadda Amurka ba ta aiki da duk wata yarjejeniya da aka cimmawa, don haka zama da ita gaba da gaba domin tattaunawa bai dace da mu ba.

Har ila yau, ya kuma ce, Shirin Iran na Nukiliya na zaman lafiya yana ci gaba da samun bunkasa saboda jagoranci na hikima na jagoran juyin juya halin musulunci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  • Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
  • Yadda Ake Tuwan Amala Da Miyar Uwaidu
  • Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
  • Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (1)
  • Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari