Aminiya:
2025-02-20@09:08:55 GMT

Gwamnatin Tinubu ba za ta hana ni magana ba — Farfesa Yusuf

Published: 13th, February 2025 GMT

Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi.

Yusuf, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa.

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’

Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce an shirya masa tuggu ne saboda dalilan siyasa.

Da yake magana yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje, ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama, kuma suna amfani da tsoffin maganganu marasa tushe.

“Ina da ƙwarin gwiwa cewa lauyoyina za su kare ni.”

Farfesa Yusuf ya kuma zargi jami’an tsaro da bibiyarsa da iyalansa.

“Tun tsawon watanni suke bin diddigin rayuwata, a zahiri da kafafen sada zumunta.

“Wannan gwamnati na amfani da hanyoyin danniya domin hana jama’a faɗin albarkacin bakinsu, kamar yadda aka saba a zamanin mulkin soja,” in ji shi.

Kama shi ya jawo ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ’yan adawa, waɗanda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin muƙushe ’yancin faɗin albarkacin baki.

Wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, sun buƙaci a saki Yusuf nan take, inda suka ce suka da adawa ga manufofin gwamnati bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba.

“Dimokuraɗiyya na buƙatar ra’ayoyi mabambanta. Amfani da tsoratarwa da shari’a don hana masu suka magana babbar barazana ce ga ’yancin jama’a,” in ji wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam.

Duk da kasancewarsa a tsare, Yusuf ya yi alƙawarin ci gaba da magana kan yadda gwamnatin Tinubu ta gaza.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da su zama masu lura da kuma neman haƙƙinsu a wajen gwamnati.

“Wannan ba batuna ne ni kaɗai ba. Batun kare ’yancin jama’a ne da hana kowace gwamnati amfani da tsoro don muƙushe al’umma.

“Dole mu tashi tsaye don kare haƙƙoƙinmu,” in ji shi.

Yanzu haka dai yana tsare yayin da kotu ta ɗage zaman sauraron buƙatar bayar da belinsa zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Farfesa Usman Yusuf gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabuwar Rundunar Tsaro A Jihar

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata.

 

A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

 

Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
  • Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususlunci A Iran IRGC Sun Bada Sanarwan Kai Hari A Kan HKI Karo Na Uku
  • Gwamnatin Niger Ta Hana Yan Najeriya Dauke Da Passpor Ta Na ECOWAS Shiga Kasar
  • Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano
  • Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro a Kano
  • Idan Rana Ta Fito, Tafin Hannu Bai Iya Kare Ta
  • Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabuwar Rundunar Tsaro A Jihar
  • Kotu ta hana Gwamnatin Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano
  • Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Daga Riƙe Wa Ƙananun Hukumomin Kano 44 Kuɗaɗensu
  • Kotu Ta Hana Gwamnatin Tarayya Riƙe Wa Kano Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi