Aminiya:
2025-02-20@08:49:04 GMT

Malaman Firamare sun sake tsunduma yajin aiki kan rashin albashi a Abuja

Published: 13th, February 2025 GMT

Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki.

Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025, sakamakon rashin biyan mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da shugabannin ƙananan hukumomi suka yi.

An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf

Shugaban Ƙungiyar NUT reshen Abuja, Kwamared Mohammed Shafas, ya bayyana cewa ƙungiyoyin sun yanke shawarar sake komawa yajin aikin ne saboda gazawar shugabannin ƙananan hukumomi shida wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi.

Ya tunatar da cewa malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi sun dakatar da yajin aiki a ranar 12 ga watan Disamban 2024 ne, bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da shugabannin ƙananan hukumomi.

Ya ce an yi yarjejeniyar ne domin fara aiwatar da biyan albashin Naira 70,000 daga watan Janairun 2025.

Sai dai, duk da hakan, shugabannin ƙananan hukumomin sun yi watsi da yarjejeniyar.

Kwamared Shafas, ya ƙara da cewa ba wai rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashin ne kaɗai ya jawo yajin aikin ba, har da gazawar shugabannin wajen biyan wasu haƙƙoƙin ma’aikata.

Ya ce buƙatun da ba a biya ba sun haɗa da kashi 40 na alawus-alawus, ƙarin albashi na kashi 25 da 35.

Ya ce, sai an biya waɗannan haƙƙoƙi kafin malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi su koma bakin aiki a Abuja.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ma aikatan Ƙananan Hukumomi malaman firamare

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1

Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
  • An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kungiyar Manyan Sakatarorin Jihar Zamfara
  • Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsaftar Muhalli 2,369
  • ASUU Reshen Jami’ar KASU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani
  • EFCC Ta Cika Hannu Da Mutane 15 Kan Zargin Zamba Ta Intanet A Abuja
  • An Gudanar Da Taron Bita Na Yini 4 Ga Malaman Tafsiri Da Ke Babura
  • Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino
  • Kotu ta hana Gwamnatin Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano
  • Kotu Ta Hana Gwamnatin Tarayya Riƙe Wa Kano Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi