Malaman Yahudawa Fiye Da 300 Sun Rattaba Hannu Akan Takardar Kin Amincewa Da Shirin Donald Trump A Yankin Gaza
Published: 13th, February 2025 GMT
Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza.
Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba.
Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan.
Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da cewa tsallake iyaka ne wacce a baya ake tsammancin cewa ba za a taba ketare ta ba, amma ga shi tana faruwa a karkashin kawancen Trump da Netanyahu.
Haka nan kuma wasikar ta fadawa Falasdinawa cewa: Sakonmu a gare ku shi ne cewa, ba ku kadai ba ne,muna a tare da ku, kuma kowane daya daga cikinsu a shirye yake ya yi yaki har kar karshen rayuwasa.
Rabbi Toba Spitzer ya bayyana abinda Trump din yake son aikatawa da cewa; “Babban zunubi ne.” Ya kuma yi tuni da abinda aka yi wa Falasdinawa a 1948 da kungiyoyin Sahayoniya masu dauke da makamai su ka kori dubun dubatar Falasdinawa daga gidajensu.
Shi kuwa Rabbi Yusuf Berman, cewa ya yi: Da alama Trump yana daukar kansa a matsayin mamallakin wannan duniya da yake da hakkin shimfida ikonsa a ko’ina a duniya.”
Haka nan kuma ya ce; koyarwar Attaura a fili take cewa; Trump mutum ne, ba shi ne mamallaki duniya ba, don haka ba shi da hakkin da zai raba Flasdinawa da kasarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন: