Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Amince Da Tiriliyan 54.9 Kasafin Kuɗin 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole.

Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita.

“A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a dawo da tattaunawar tsagaita bude wuta da kuma kai kayan agaji a Gaza ba tare da wata tangarda ba.

Ya yi ishara da jawabin da babban jami’in agaji na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya yi wa UNSC a farkon wannan makon, inda yace yin aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ita ce hanya mafi dacewa domin kare fararen hula  a Gaza, da kuma sako wadanda aka yi garkuwa da su, gami da shigar da kayan agaji da kayayyakin bukatar rayuwa zuwa Gaza.

Khari ya ce jami’an MDD shida na daga cikin daruruwan mutanen da aka kashe tun bayan da Isra’ila ta sake dawo da kai hare-hare a ranar Talata.

A daya bangaren kuma Majalisar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da “rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwa da  jikkatar fararen hula masu yawa a hare-haren jiragen saman Isra’ila a baya-bayan nan”.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru Amirul Hajj Na Shekarar 2025
  • Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha
  • Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza
  • Ƴansandan Sun Gayyaci Sanata Karimi Kan Zargin Shigar Kungiyar Leƙen Asirin Rasha Majalisa’
  • Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo
  • Dalilan Gwamnatin Tarayya Na Zuba Naira Tiriliyan 1.5 A Bankin Aikin Noma -Kyari
  • Fashin Baki Kan Kasafin Kudin 2025 Na Naira Tiriliyan 54.99
  • Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas
  • MDD da EU sun yi tir da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila ta yi
  • Ribas: Ba mu karɓi sisin kwabo domin amincewa da dokar ta baci ba – Majalisar Wakilai