Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9
Published: 13th, February 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin.
Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka shafi huldar kasa da kasa ga shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar.
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususlunci A Iran IRGC Sun Bada Sanarwan Kai Hari A Kan HKI Karo Na Uku
Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar. Ya kuma kara da cewa, zasu kai harin don haka HKI da Amurka kawo mata yaki.
Yace wadan nan kasashe suna neman yaki da JMI, amma mafi yawan shirin nasu na farfaganda ne. Amma dolene mu shiga yaki don mu hana yaki faruwa. Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran suna yaki ne don ladabtar da HKI don ta gane cewa JMI ba mai sauki. Sannan yakamata ta sani kuma Amurka ta sani dare da rana ayyukan kera makamai suna tafiya a cikin kasar.