Aminiya:
2025-02-20@08:57:42 GMT

’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025

Published: 13th, February 2025 GMT

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025.

Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar.

An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas

Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025.

Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya.

Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, bayan tuntuɓar shugabannin hukumar a jihohi da wakilin fadar shugaban ƙasa.

Shugaban ya tabbatar da ƙulla yarjejeniya da waɗanda za su kasance masu hidima tun da wuri don guje wa fuskantar tsaiko.

Wannan matakin yana da muhimmanci saboda ana sa ran fara aikin samar da biza ga maniyyata daga ranar 19 ga watan Fabrairu.

Shugaban NAHCON ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, bisa goyon baya da taimakon da yake bai wa hukumar.

Ya ce hukumar za ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa maniyyata sun samu damar yin Hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.

Ya kuma buƙaci su ci gaba da bibiyar kafofin sadarwa na NAHCON don samun sabbin bayanai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Farfesa Pakistan Kasar Saudiyya tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba

Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya.

Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba.

 Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan ne.”

Bugu da kari Trump ya ce, ko kadan bai kamata a ce yaki ya barke ba, domin yaki ne da babu yadda za a yi ya yi nasara ba tare da goyon bayan Amurka da kuma Trump ba, yana mai yin ishara da cewa, ahalin yanzu Amurka tana tattaunawa cikin nasara da Rasha domin kawo karshen yakin.”

Wani sashe na sakon Trump din ya kunshi cewa; Ina son kasar Ukiraniya, sai dai abinda Volodymyr Zelenskyy ya yi, ya munana, ya ruguza  kasarsa, kuma miliyoyin mutane sun mutu ba tare da dalili ba.

A gefe daya, kasashen turai sun mayar da martani akan maganganun na Trump, inda shugaban gwamantin Jamus ya ce shugaban kasar ta Ukiraniya ba dan dan kama-karya ba ne.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
  • NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
  • Zargin Daukar Nauyin Boko Haram: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Akpabio A Villa
  • Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa: Barazanar Makiya Kan Iran Ba Zata Yi Nasara Ba
  • Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya
  • NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar
  • FG Ta Jaddada Bukatar Samarda Sabbin Ka’idojin Visa Domin Taimakawa Kasuwancin A Duniya
  • Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU
  • Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu