Liyafar Bikin Fitilu Na 2025 Ta CMG Ta Samu Yabo Sosai
Published: 14th, February 2025 GMT
An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara.
A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke karkashin CMG, ta tallata tare da watsa rahotanni masu alaka da liyafar cikin harsuna 82, haka kuma tashar CCTV ta watsa shirye shiryen liyafar masu ban sha’awa ga kafofin yada labarai na duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Talabijin Na Kasar Sin Masu Inganci A Malaysia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp