Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6.

An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don sayar da kayayyakin daddadun kantuna.

Daga cikin su kuma, kasuwannin kayayyakin da ake yawan sayen su a lokacin bikin bazara guda goma, sun samu yawan kudin tallace-tallace kai tsaye sama da yuan miliyan 500, kuma sun inganta kashe kudi ta yanar gizo da kuma ta zahiri sama da yuan biliyan 1.6, musamman kudin da aka kashe kan abincin daddadun kantunan ya karu da kashi 13.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara.(Safiyah Ma)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kayayyakin da

এছাড়াও পড়ুন:

UNICEF Ya Bukaci Hadin Kai Don Inganta Rayuwar Kananan Yara A Jigawa

Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma.

Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin.

Ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su bayar da gudunmawarsu wajen bada gudunmawarsu  domin magance halin kuncin rayuwa da kananan yara ke ciki a jihar Jigawa, ta hanyar amfani da kwararan hujjojin da za a yi amfani da su domin tsara bangarori daban-daban.

Ya ce binciken ya nuna cewa kashi 90 bisa 100 na yara a jihar Jigawa suna fama da matsanancin  kangin talauci, yayin da kimanin kashi 86 bisa 100 ke fuskantar rashi a fannoni masu muhimmanci da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da abinci mai gina jiki, da tsaftataccen ruwan sha, da sauransu.

Mista Farah ya bayyana bukatar hada hannu cikin gaggawa domin rage radadin talauci da inganta rayuwar yara a jihar Jigawa.

“Don karfafa kokarinmu na hadin gwiwa, muna neman goyon bayan gwamnati wajen samar da matakan da za su tabbatar da yin amfani da bayanan da aka samu na kananan hukumomi domin gudanar da abin da ya dace”.

“Sauran fannonin sun hada da amincewa da ƙayyadaddun manufofin kare lafiyar jama’a, da amincewa da daftarin dokar kare al’umma da aka yi wa kwaskwarima zuwa doka, da ƙara yawan kason kasafin kuɗi don shirye-shirye na musamman na yara, da tabbatar da yin rajistar haihuwa ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar“, in ji Farah.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
  • UNICEF Ya Bukaci Hadin Kai Don Inganta Rayuwar Kananan Yara A Jigawa
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
  • Da Muguwar Rawa, Gwamma Kin Tashi
  • Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
  • An Kaddamar Da Bikin “Tafiya A Kasar Sin Bisa Ga Fina-finan Kasar”
  • Jagora : Kokarin Makiya Na Haifar Da Sabani Ya Ci Tura
  • Iran Za Ta Aike Da Tawaga A Matakin Koli Don Halartar Jana’izar Nasrallah
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Tituna Akan Kudi Naira Biliyan 6.3