Amurka ta kakaba wa babban mai shigar da kara na kotun ICC takunkumi kan binciken laifukan yakin Isra’ila
Published: 14th, February 2025 GMT
Amurka ta kakaba takunkumi kan babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da binciken da kotun ta ICC ke yi kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra’ila a Gaza da sojojin Amurka.
Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakabawa Karim Khan takunkumi a matsayin martani ga umarnin shugaba Donald Trump na ranar 6 ga watan Fabrairu, wanda ya bukaci a sanya masa takunkumi.
Trump ya yi iƙirarin cewa kotun ta ɗauki “haramtakan da ba su da tushe balle makama” akan Amurka da Isra’ila.
Kamar yadda aka ba da umarnin, shugaban na Amurka a yanzu yana da iko mai yawa na daskare kadarorin da kuma sanya takunkumin tafiye-tafiye kan ma’aikatan ICC da iyalansu. Za a sanya takunkumin ne idan Washington ta yanke shawarar cewa ma’aikatan na da hannu a yunkurin bincike ko gurfanar da Amurkawa da wasu kawayen Amurka ciki har da Isra’ilawa.
Tare da binciken da ta yi kan “Isra’ila”, kotun ta ICC tana duba laifukan yaki da cin zarafin bil’adama da suka faru a lokacin mamayar da Amurka ta yi wa Afganistan daga 2001 zuwa 2021.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa.
Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya ce shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai ziyarci Tehran a ranar Laraba.
Gharibabadi ya bayyana cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, zai gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami.
Ya kara da cewa “ziyarar na cikin tsarin ci gaba da hulda da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.”
Ziyarar ta shugaban hukumar ta IAEA za ta zo ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke shirin gudanar da tattaunawar ta biyu, wanda Oman ta shiga tsakani a ranar Asabar data gabata.