Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya
Published: 14th, February 2025 GMT
Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu.
Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya.
Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa.
Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau.
2007Sai dai tun ba a je ko’ina ba, suka samu saɓani da Malam Ibrahim Shekarau kan shugabancin jam’iyyar, wadda da ta koma ANPP.
Hakan ta sa duk da bai fita daga jam’iyyar ba, Ɗan Zago, da ƙungiyarsa ta “Zago Aƙida” ba su goyi bayan tazarcen Shekarau ba a zaɓen 2007.
Sannan kuma, kusancin Ɗan Zago da Buhari ta sa Buhari bai je Kano yi wa Shekarau kamfe ba.
2011Gabanin zaɓen 2011, Ahmadu Haruna zago, ya bi tawagar Buhari wajen ficewa daga ANPP tare da kafa sabuwar jam’iyya ta CPC.
Shi ne ya shugabanci jam’iyyar a mataki na riko.
Sai dai daga baya, an yi ta samun rikicin shugabancin jam’iyya tsakaninsa da wasu ’yan CPC a Kano.
2015Jam’iyyun ANPP, CPC, ACN, sun haɗe da ’yan G-5 na Jam’iyyar PDP, irin su Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wajen kafa sabuwar jam’iyyar APC.
A wannan lokaci ne, Ɗan Zago, karon farko ya bar Buhari, ya goyi da bayan Kwankwaso a zaɓen cikin gida na takarar shugabancin ƙasa.
Hakan ta sa duk da ɗawainiyar tallata Buhari da yanyi na tsawon shekaru, bai amfana da gwamnatinsa ba.
2019A gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Ahmadu Zago ya riƙe muƙamin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin noma.
2023Bayan ƙarewar wa’adin shugaban jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas, Ɗan zago, ya nuna sha’awarsa ta fitowa takara.
Sai dai zaɓen ya bar baya da ƙura, domin sai da aka yi ta fama a kotu, yau a ce Ɗan Zago ne, gobe a ce Abdullahi Abbas ne. Abin da ya raba kan jam’iyyar APC biyu a Kano.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Barau I. Jibril da Malam Ibrahim Shekarau da Sha’aban Ibrahim Sharada, su ne a ɓangaren Ahmadu Zago, yayin da gwamnatin Ganduje ta ce Abdullahi Abbas, shi ne ya sake cin zaɓen shugabancin jam’iyyar APC a karo na biyu.
Duk da Ahmadu Zango bai bar jam’iyyar APC ba, shi da jama’ar sa ta “Zago Aƙida” sun sha fitowa rediyo, suna barranta kansu da duk wata tafiyar siyasa da take da alaƙa da Ganduje.
Bayan lashe zaɓe da Abba Kabir Yusuf ya yi, ya baiwa Alhaji Ahmadu Haruna Zago, shugabancin hukumar kwashe shara ta Jihar Kano (REMASAB), matsayin da yake riƙe da shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Ya mutu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama.
Baya ga siyasa, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, sanannen ɗan kasuwar canji ne, a kasuwar canjin kuɗi ta Wafa da ke Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ahmadu Haruna Zago Ahmadu Haruna zago jam iyyar APC jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma.
’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasuA cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta.
Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta hanyar riƙe kyawawan halayenta na gaskiya da nagarta.
Gwamnan Gombe, ya kuma miƙa ta’aziyyar gwamnatinsa da mutanen jiharsa, ta hanyar addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya kuma sa Aljanna Firdausi ta zama makomarta.