HausaTv:
2025-02-20@08:54:46 GMT

Afirka ta Kudu: Ba Za Mu Janye Kararmu Kan Isra’ila A Kotun ICJ Ba

Published: 14th, February 2025 GMT

Afirka ta Kudu ta yi alkawarin ci gaba da shari’ar kisan kiyashi da ta shigar a gaban kotun ICJ a kan Isr’ila,  duk da umurnin da Donald Trump ya bayar na katse taimakon da Amurka ke ba kasar Afirka ta Kudu saboda matakin da ta dauka kan babbar kawar Amurka.

“Babu wata dama” kan janye karar ta  ICJ, ba tare da la’akari da duk wata barazana ko mataki da Trump zai dauka ba, a cewar ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola, wanda ya kara da cewa, “Tsayawa a kan ka’idojinmu wani lokaci yana da sakamako, amma mun tsaya tsayin daka kan wannan batu, ganin cewa yana da muhimmanci ga duniya, da kuma bin doka da ka’ida.

Dokar da Trump ya sanya wa hannu ta dakatar da ba da taimako ga Afirka ta Kudu, ya kuma yi alkawarin ci gaba da daukar wasu matakan domin takura kasar Afirka ta kudu kan matakin shigar da kara da ta dauka a kan Isra’ila game da batun yakin Gaza.

Afirka ta Kudu ta gabatar da karar kisan kiyashi kan “Isra’ila” a karshen shekara ta 2023 zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, inda ta bukaci kotun kasa da kasa da ta dauki matakai kan mahukuntan Isra’ila saboda karya yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ireland a hukumance ta shiga cikin shari’ar Afirka ta Kudu a watan Disamba 2024, kuma jim kadan bayan haka, Cuba ta sanar da aniyar ta na shiga cikin lamarin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya fadawa Turawa Kan Cewa Basa Cikin Tattaunawa Kan Tsagaita Wuta A Ukraine

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine. Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa. Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu. Mr Vances ya bayyana hakane a taron tsaro da ke gudana a birnin Munich.  

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
  • Sin Ta Tabbatar Da Goyon Bayanta Ga Kafa Kasashe Biyu Ga Isra’ila Da Palasdinu
  • Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump
  • Shugaban Amurka Ya Ce: Sun Baiwa Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Damar Ya Aikata Abin Da Yake So
  • Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya
  • Janye Tallafin Amurka Ya Jefa Masu Fama Da Cutar HIV A Kasar Afirka Ta Kudu Cikin Fargaba
  • Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU
  • Hamas Ta Yabawa Tarayyar Afirka Kan Yin Tir Da Kisan Kare Dangin Isra’ila A Gaza
  • Trump Ya fadawa Turawa Kan Cewa Basa Cikin Tattaunawa Kan Tsagaita Wuta A Ukraine
  • Amurka Da Isra’ila Sun Sake Barazanar ‘Lugudan Wuta’ A Gaza