Pezeshkian: Iran za ta magance matsalolinta ne ta hanyar dogaro da kanta
Published: 14th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa makiya kasarsa suna neman murkushe al’ummar kasar ta hanyar takunkumi da barazana.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da masana da masu fada aji na lardin Bushehr da ke kudancin kasar a ranar Alhamis , inda ya ce “Makiya suna son mu ulakanta a gabansu ta hanyar takunkumi da barazana, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, kuma za mu magance matsalolinmu ta hanyar dogaro da jama’a.
Ya yi kakkausar suka kan irin matakan da Amurka ke dauka a kan Iran wadanda suke karo da juna, yana mai cewa shugaban Amurka Donald Trump na ikirarin cewa yana son tattaunawa da Iran amma a lokaci guda ya kakabawa Tehran takunkumi mafi tsauri.
“Ba ma son wani ya sanya mana takunkumi,” in ji Pezeshkian, ya kara da cewa, “Ba wai idan Amurka ta kakaba mana takunkumi ba, ba za mu iya yin komai ba. Za mu tafiyar da kasar ta hanyar dogaro da karfin cikin gida.”in ji Pezeshkian.
Ya nanata manufofin Iran na yin mu’amala da dukkan kasashe cikin lumana da ‘yan uwantaka, yana mai jaddada cewa, “Muna kokarin kulla kyakkyawar alaka da abokantaka da makwabta.”
Shugaban ya kara da cewa hadin kai, mu’amala da tsare-tsare na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin cikin gida.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Iraniyawa Saboda Amfanin Kasar
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da sauransu. Sannan yayi fatan sabuwar shekara ta 1404 mai albarka ga mutanen kasar da kuma sauran masoya.