Masu noman tabar wiwi na barazanar ƙona gidajenmu —Makiyaya
Published: 14th, February 2025 GMT
Makiyaya sun koka bisa abin da suka kira tsangwama da tsana da wasu manoman tabar wiwi ne suke nuna musu tare da yi musu barazanar ƙone gidajensu a inda suke zaune shekaru aru-aru.
Makiyaya Fulani sun yi ƙorafi ne bayan manoman tabar wuri sun kafa musu ƙahon zuƙa a inda suke zaune a yankin Oja-Badun da ke Ƙaramar Humumar Eleyele a Jihar Oyo, daura da garin Ogumaki na Jihar Ogun.
Shugaban Fulanin yankin, Alhaji Muhammadu Wakili ya shaida wa Aminiya cewa, jagoran manoman tabar wiwi a yankin ya sa wa Fulani makiyayan karan tsana, bayan da suka bai wa jami’an tsaro bayanan cewa, suna noma tabar wiwi a yankin.
Ya ce lamarin ya kai ga ’yan sanda sun kama yaran mutumin a gonar tasa, kuma tun daga lokacin shi da abokan sana’arsa suka uzzura musu.
Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyya An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a KatsinaWakili ya ce, “kimanin wata huɗu ke nan da muka bai wa ’yan sanda bayanin cewa, ana noma tabar wiwi a yankin da muke kiwo, kuma a wannan lokacin ’yan sandan sun yi nasarar kama mutum guda a gonar, wanda yaron mutumin ne.
“Tun daga lokacin suke nuna mana tsangwama, inda a makon jiya suka kashe mana shanu 12, baya ga barazanar da suke yi mana na cewa, sai sun tashe mu bayan sun ƙone mana gidaje.
“A ranar Asabar ɗin da ta gabata suka yo zuga, suka nufo rugarmu za su ƙona, amma da taimakon Allah, DPO na ’yan sandan yankin ya kawo mana ɗauki shi da jami’ansa, suka fatattake su, suka hana su yunƙurin nasu na ƙona mana gidaje.”
Wakili ya ƙara da cewa, mutanen sun daɗe suna yi masu barazana, inda suke goranta masu cewa, a baya sun ƙone masu gidaje shekaru huɗu da suka shuɗe, kuma babu abin da aka yi, don haka a yanzu ma za su sake domin babu abin da za a yi.
“Sun taɓa ƙone mana gidaje shekaru huɗu da suka wuce, shi ne yanzu suke yi mana izgilanci, suna barazanar za su sake kuma babu abun da za a yi, kuma daman kafin su kai ga kawo mana farmaki a ranar Asabar da ta gabata, shi wannan mutum ya je gidan radiyo, inda ya faɗi bayanan ƙarya a kanmu da ’yan sanda, cewa muna ɓata musu gona.
“Idan har da gaske mun shiga gonarsu mun lalata ai akwai hukuma, sai su nuna wa ’yan sanda, su ga ɓarnar da aka yi masu, amma babu ko alama, amma mu shanun da suka kashe mana da harbin bindiga da sara duk mun kai ƙara wajen ’yan sanda kuma muna da hotunansu, kuma ko a baya can yaran mutumin sun harbar mana yaranmu Fulani da ke kiwo a daji, inda suka harbe su da bindiga a ƙafa, sai da muka kai su asibiti, aka cire masu harsashi.
“Duk wannan tsangwamar da suke mana so suke mu bar wajen don su samu, su sake su ci gaba da noman tabar wiwi kamar yadda suka saba, domin sun sha alwashin sai sun kore mu daga wajen da muke zaune shekaru aru-aru.
“Tun lokacin mulkin Gowon, muke zaune lafiya a wannan yankin, ba mu da matsala da al’ummar yankin da shugabanninsu da ma jami’an tsaro domin tare muke aiki, muna ba su haɗin kai.
“Mutanen da muke da matsala da su kuma duk lokacin da aka sami akasi shanunmu suka yi ɓarna a gona, muna zuwa a tattauna a sasanta, mu a biya diyya, don haka masu noman tabar wiwni nan kaɗai ne ke tsangwamar mu, suna cewa sai sun kore mu za su sami damar yin noman tabar wiwi yadda suke so,” in ji shi.
Sarkin Fulanin na Oga Badun ya ƙara da cewa, bayan barazanar ƙone masu gidaje da mutanen suka yi, DPO ’yan sandan yankin ya hana su, ya gayyaci ɓangarorin zuwa taron zaman lafiya a yankin a ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Sai dai kin lokacin Shugaban Ƙaramar Hukumar Eleyele ya buƙaci a yi taron a gidansa a ranar Litinin mai zuwa domin kawo ƙarshen matsalar.
“Mu Fulani a wannan yankin muna aiki tare da masu gari da jami’an tsaron ’yan sanda da na Amotekun don tabbatar da tsaro, kuma haɗin kan da muke bayarwa suna ba mu, mu ma,” in ji shi.
Muhammed Farouk shi ne sakataren Fulani makiyaya mazauna yankin Oja-Badun ya bayyana cewa, suna ƙoƙarin ganin an sami zaman lafiya shi ya sa suke bai wa ’yan sanda da Amoteku da sauran al’ummar gari haɗin kai, “komai tare ake yi da mu na ci-gaban gari duba da daɗewar da muka yi a nan.
”Amma yanzu kuma masu noman tabar wiwi su ne suka sako mu a gaba, don haka muna kira ga mahukunta da su zo su yi bincike, su kawo mana ɗauki,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tabar wiwi noman tabar wiwi
এছাড়াও পড়ুন: