Jami’ar Tarayya Ta Lafiya Ta Rantsar Dalibai Dubu 8
Published: 14th, February 2025 GMT
Jami’ar Tarayya ta Lafia ta yi bikin rantsar dalibai 8,000 da suka sami gurbin karatu a sassan 76 a tsakanin tsangayoyin jami’ar 12.
Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya sake jaddada matsayar hukumar a kan duk wani nau’i na rashin da’a da kuma shiga kungiyoyin asiri.
Shugaban jami’ar wanda mataimakin shugaban jami’ar na sashen koyarwa, Farfesa Alemchi Chuku ya wakilta ya ci gaba da cewa basu da hakuri ga duk wani nau’i na rashin da’a kuma za su yi kakkausar suka ga munanan dabi’u.
Ya kuma bukaci sabbin daliban da su mutunta juna da kuma ma’aikatan jami’ar da malamai na jami’ar domin ganin zamansu ya kasance mai amfani.
“Ba mu yarda da ayyukan kungiyoyin da suka saba wa zamantakewa ba, musamman duk wanda aka kama yana gudanar da ayyukan kungiyar asiri za a kore shi daga jami’ar.
COV/Aliyu Muraki/Lafia./Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a kudu maso yammacin Nijar
Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata.
Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin da aka kai a kauyen Fonbita da ke cikin kauyan Kokorou dake jihar Tillabery wanda ya faru a lokacin da wasu ‘yan ta’addan na kungiyar Da’ish a yankin Sahara (ISGS) suka far wa masallacin, inda suka auka wa masu ibada dake sallar Juma’a.
Baghaei ya bayyana cewa, wannan ta’addancin da aka aikata a lokacin sallar Juma’a ya saba wa ka’idar Musulunci, kuma ya saba wa dukkanin ka’idojin shari’a da hakkin dan Adam na kasa da kasa.
Kakakin na Iran ya jaddada muhimmancin kara inganta hadin gwiwa a matakai daban-daban na shiyya-shiyya da na kasa da kasa don dakile da yaki da ta’addanci.
Ya zama dole a gurfanar da masu hannu a harin ta’addanci da kuma hukunta su.
Baghaei ya nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da gwamnati da kuma al’ummar Nijar kan harin ta’addanci.