Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-02-20@09:12:52 GMT

NUJ Ta Dukufa Wajen Kula Da Jin Dadin ‘Yan Jarida

Published: 14th, February 2025 GMT

NUJ Ta Dukufa Wajen Kula Da Jin Dadin ‘Yan Jarida

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya.

 

Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar.

 

A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don tabbatar da tafiyar da harkokin kungiyar cikin sauki.

 

Har ila yau, ta ce, mambobin CWC sun yaba wa shugaban NUJ bisa hangen nesansa kuma sun bukace shi da ya ci gaba da ci gaba da ciyar da manufofin kungiyar gaba.

 

Sanarwar ta yi bayanin cewa, kungiyar za ta shirya taron karawa juna sani na horar da ‘yan jarida guda biyu a cikin rubu’in farko na shekara don bunkasa sana’o’i a bangarori daban-daban na harkar yada labarai.

 

Domin tabbatar da gaskiya wajen fitar da kudaden rajista, kungiyar na tattaunawa da ofishin biyan albashi na zamani na tarayya (IPPIS) domin tabbatar da cewa duk kudaden da aka cire daga mambobin kungiyar NUJ ana tura su kai tsaye zuwa asusun NUJ.

 

CWC ta yabawa gwamnatin jihar Kebbi kan ci gaban ababen more rayuwa da suka hada da titunan gari, filin ajiye motoci na zamani, zuba jarin noma, da tsare-tsare na jin dadin jama’a, ya kuma bukaci gwamnan da ya ci gaba da gudanar da wannan kokari na ganin ya cika aikin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na dan kungiya.

 

Kungiyar ta NUJ ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da fadin kasar nan na noma domin bunkasa samar da abinci sannan kuma ta yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen magance kalubalen tsaron da ke addabar al’ummar kasar, haka ma gwamnati ta ba da fifikon jin dadin ‘yan kasa wajen tsara manufofi.

 

PR/Abdullahi Tukur/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

ASUU Reshen Jami’ar KASU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani

“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025.

 

“Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas Ta Ce Tana Iya Sakin Dukkan Fursinonin Yahudawa Gaba Daya A Lokaci Guda
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Watsi Da Karin Shuruddan Gwamnatin ‘Yan Sayoniyya Kan Tsagaita Bude Wuta
  • An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kungiyar Manyan Sakatarorin Jihar Zamfara
  • ASUU Reshen Jami’ar KASU Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani
  • Hamas: Za A Mika Gawawwakin ‘Yan Mamaya Da Kuma Fursunoni Rayayyu A Ranakun Alhamis Da Asabar
  • IRGC Ta Sanar Da Rusa  Kungiyar “Yan Leken Asirin Amurka Da HKI A Iran
  • Jagora Ya Gana Da Shuwagabannin Kungiyar Jihadul Islami A Nan Tehran
  • Nijar Na Son Kulla Yarjejeniya Kafofin Yada Labarai Na Iran
  • Hamas Ta Yabawa Tarayyar Afirka Kan Yin Tir Da Kisan Kare Dangin Isra’ila A Gaza
  • Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu