Sharhi Kan Dabarun Noman Dabino A Nijeriya
Published: 14th, February 2025 GMT
Duk da cewa, ana kara samun yin nomansa da yawa, ana kuma ci gaba da samun karancinsa, musamman saboda yadda al’umma ke kara bukatarsa.
Kamar Ban Ruwa Nawa Bishiyar Dabino Ke Bukata?
Dabinon da aka shuka, bai cika bukatar a dinga yi masa ban ruwa bayan an shuka shi ba, musamman a lokacin kakar damina.
A Wane Yanayi Dabino Yake Girma?
Dabino ya fi yin girma a yanayin zafi, haka nan kuma ya fi yin kyau a kasar noma ta kasar Amurka da ake samun rana mai zafi.
Kamar Zufin Rami Nawa Dabino Ke Bukata?
Yana girma a zurfin ramin da ya kai kafa daya zuwa kafa sha daya tare kuma da santi mita daga talatin zuwa arba’in da biyar, wannan ya danganta da irin ingancin kasar noman da aka shuka shi da kuma irin yanayin, haka nan; yana kai wa daga tsawon shekara 15 zuwa 20 kafin ya kammala girma.
A duk fannin duniya, Nijeriya ce kawai ke nomansa sau biyu a shekara, har Nahiyar Afirka ta Arewa da Gabas ta tsakiya, inda ake hasashen Dabinon ya samu asali, sannan ana yin nomansa ne a kakar noma daya.
Dabinon da aka shuka, na fara fitar da fure ne daga watan Janairu zuwa watan Fabirairu, inda kuma yake kammala nuna daga watan Yuni zuwa watan Oktoba.
Wanda kuma aka shuka a kakar noman damina, yana fara yin fure ne daga watan Satumba zuwa watan Oktoba, inda kuma yake kai wa munzalin a girbe shi daga watan Fabirairu zuwa watan Maris.
Batun Shuka Shi:
Ana amfani da Iri don shuka shi ko kuma a shuka Saiwarsa wacce ke girma zuwa Bishiya.
Ana kuma yanko Saiwar ce daga jikin Bishiyar da ta kai daga shekara hudu zuwa biyar, inda kuma ake fara shuka shi daga watan Juli zuwa watan Satumba, haka a kadada daya ana iya samun Bishiyar Dabino kimanin 150.
Gyaran Gona:
Ana so a gyra gonar da za a shuka Dabino kafin ruwan damina ya fara sauka, inda ake so a yi wa gonar haro; domin ta samu danshi sosai.
Zuba Taki:
An fi so a zuba masa takin gargajiya da ke dauke da sindarin ‘Nitrogen’, musamman domin ya yi saurin girma.
Ban Ruwa:
Bishiyar Dabino na jurewa kowane irin yanayi na noma, an fi so a yi masa ban ruwa, musamman a lokacin rani.
Cire Ciyawa:
Ana bukatar manomi ya tabatar ya kiyaye wajen yin noma, musamman don gudun kada ya kamu da cututtuka ko harbin kwari.
Lokacin Yin Girbi:
Ana yi masa girbi ne bayan ya kammala girman baki-daya, wato daga shekara 15 zuwa shekara 20.
Adana Shi Bayan Girbi:
Sabon Dabinon da aka girbe, ana adana shi a cikin na’ura mai sanyi daga sati biyu zuwa uku, ana kuma iya adana shi har zuwa tsawon wata hudu.
Hada-hadar Kasuwancinsa:
Dabino ne yake tallan kansa da kansa, musamman ganin cewa, jama’a na kara bukatarsa, kana ana sarrafa shi zuwa nau’ikan wasu abin sha; kamar kunun Aya da sauran makamantansu.
Daga Tsawon Kafa Nawa Bishiyar Dabino Ke Girma?
Bishiyar Dabino na kai wa tsawon kafa 20, banda ganyensa; yana kuma kai wa tsawon shekara daga 15 zuwa 20 kafin ya kammala girman.
Har ila yau, Dabinon da ya kai tsawon shekara 100, yana iya kai wa tsawon kafa 100.
Ana Samun dimbin Riba A Noman Dabino
A shekarar 2020, Kalifoniya ta samar da tan 49,300 da aka noma kadada 12,500, inda kuma a duk kadada daya aka noma tan 3.94 da kudinsa ya kai dala 2,320 na kowane tan daya. An kuma kiyasta yawan amfanin Dabinon da cewa; ya kai dala miliyan 114.
কীওয়ার্ড: Bishiyar Dabino Bishiyar da
এছাড়াও পড়ুন:
Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye.
Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya.
Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne.
A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp