Aminiya:
2025-03-23@03:44:35 GMT

Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa

Published: 14th, February 2025 GMT

Hakan dai ya faru ne dalilin baiko da fitaccen mawaƙin ya yi da ’yar majalisar jiha mai wakiltar Egor a jihar Edo, Natasha Osawuru, a wani bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya.

Ɓullar bidiyon ke da wuya mahaifiyar 2Face, Rose Idibia, ta fito a wani bidiyo tana roƙon duk wata uwa ta taya ta roƙon ‘yar majalisar ta karya asirin da ta yi wa ɗanta.

Kalaman mahaifiyar tasa dai na da nasaba da rabuwar 2Face da matarsa Annie da har yanzu bai kammala ba a hukumance.

Mahaifiyar tasa ta ce rashin haƙurin jiran aurensa ya rabu da tsohuwar matar tasa, da gaggawar neman auren ‘yar majalisar ne ya sanya ta gano cewa ɗan nata ba a hayyacinsa ya ke ba.

Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano Masu noman tabar wiwi na barazanar ƙona gidajenmu —Makiyaya

Tun kafin auren 2Face da Annie wacce tsohuwar jarumar Nollywood ce sun sha yamutsa hazo, musamman haife-haife da 2Face ɗin ya yi da wasu matan biyu, duk da cewa suna tsaka da soyayya a lokacin.

Kazalika bayan auren rahoton soyayya da wasu matan bai tsaya ba, baya ga rigingimu tsakanin danginsa da Annie, da kuma zargin da ɗan uwanta ya yi mata na jefa shi a hanyar shaye-shaye.

Rahotanni dai na nuna sai da 2Face ya haifi ‘ya’ya huɗu da wasu matan kafin su yi aure, sannan suka haifi na biyar ɗin tare.
Idan za a iya tunawa dai, makonni da suka gabata ne 2Face ɗin ya fito ya ce zai rabu da tsohuwar matarsa Annie baya shekaru 12 da aure.

Sai dai daga baya ya fito ya ce masu kutse ne suka aikata hakan, bayan abokanan aikinsa da dama sun fito sun yi Alla-wadai da fito da zancen soshiyal midiya.

Kwanaki kaɗan bayan nan ne kuma ya sake yin bidiyo ya ce babu wani kutse da aka yi wa shafinsa, shi ne ya rubuta da kansa.
Jaridar Punch ta rawaito tsohuwar matar 2Face ɗin na wani wurin gyaran hali yanzu haka saboda fama da matsanancin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ta ke yi, kuma fitacciyar mawaƙiya Tiwa Savage na daga cikin masu kula da ita.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Natasha Osawuru Nollywood

এছাড়াও পড়ুন:

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]

● Ta biyu, yana nuna rashin ladabi ga Allah, domin ainihin hassada ita ce jin haushin yadda Allah Ya ba wa wani ni’ima, kuma hakan yana nufin yana sukar hukuncin Allah.

● Ta uku, zuciyarsa tana shan wahala saboda yawan damuwa da baƙin ciki.”

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [14] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]

Fashin Baƙi:

Ibn Juzai Allah Ya ji ƙan sa, ya yi cikakken bayani kan illolin hassada ga mai hassada ta hanyoyi guda uku: samun zunubi, da rashin ladabi ga Allah, da wahalar da zuciya.

Zan ɗan yi bayani a kan waɗan gaɓoɓi guda uku da malam ya ambata, tare da hujjoji daga Alƙur’ani, da Hadisi, da mahangar masana ilimi. Ga maganar kamar haka:

Hassada Zunubi Ce Kuma Haramun Ce a Shari’a:

A Musulunci, hassada tana daga cikin manyan zunubai. Dalili kuwa shi ne cewa tana ƙunshe da ƙiyayya da kishi mara dalili. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:” Shin yanzu za su riƙa yi wa mutane hassada ne a kan abin da Allah Ya ba su na falalarsa?” Suratun Nisã’i aya ta 54. Ma’anar wannan aya ita ce: idan mutum yana jin haushin wani saboda wata ni’ima da Allah Ya ba shi, to yana fuskantar hukuncin Allah da kishi maras tushe. Haka nan Annabi (SAW) ya fadi a cikin hadisi cewa: “Kada ku yi hassada“ Bukhari da Muslim ne ya ruwaito.

Me Yasa Hassada Take Zama Zunubi?

Hassada ta zama zunubi ne ta fuskoki masu yawa.

• Akwai saɓa wa Allah da Manzonsa (S.A.W) na hani a kan hassada.
• Hassada tana sa mutum ya yi mummunan zato ga Allah, yana ganin kamar bai dace Allah Ya ba wani wata ni’ima ba.
• Hassada tana iya sa mutum ya aikata mugun aiki, kamar cutar da wanda yake yi wa hassada.
• Hassada tana hana mutum mai da hankali kan nasararsa, tare da an giza shi yana riƙa jin haushin wasu maimakon yin aikin da zai amfane shi.
• Hassada tana hana mutum gode wa Allah da abin da yake da shi.

Mafita:
Maimakon haka, Musulunci ya na koyar da yin gibḍa (kishi mai kyau), wato yin burin yin abin da wani yake yi ba tare da fatan sharri gare shi ba. Misali, idan mutum yana ganin wani ya fi shi ilimi, maimakon yin hassada, yana da kyau ya yi addu’a Allah Ya ba shi ilimi kamar nasa.

Hassada Rashin Ladabi Ce Ga Allah:

Idan mutum yana jin haushin yadda wani ya samu wata ni’ima, hakan yana nufin yana ƙin hukuncin Allah ne. Wannan kuwa yana iya jefa mutum cikin shakka ko rashin yarda da Allah. Allah Ta’ala Ya ce a cikin Alƙur’ani: ”Kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai Yalwa ne, Masani” Suratul Baƙara aya ta 247.

A ma’anar wannan aya ita ce, Allah ne yake rarraba arziki, da ilimi, da kyau, da sauran ni’imomi ga wanda Ya ga dama. Idan mutum yana jin haushin wannan, to yana sukar hukuncin Allah ne. Misali a rayuwa, Idan mutum yana jin haushin wani saboda yana da dukiya, wannan yana nuna cewa bai gamsu da yadda Allah ke bayar da arziki ba. Idan mutum yana jin haushin wani saboda yana da kyau ko hikima, yana nufin yana ƙin tsarin Allah ne. Hassada tana sa mutum ya yi tambayoyi marasa amfani, kamar:

○ Me yasa Allah Ya ba wane, amma ni bai ba ni ba?”
○ Me yasa ni ban samu kaza ba alhali na fi shi ƙoƙari?
Waɗannan tunani suna iya jefa mutum cikin gaba da ƙaddara, wanda hakan yana daga cikin munanan al’amura a Musulunci da suke taɓa imanin bawa.

Hassada Tana Jefa Mai Yi Cikin Wahalar Zuciya da Damuwa:

Baya ga kasancewar hassada zunubi, hassada tana cutar da zuciyar mai yi. Wannan yana da nasaba da ilimin halayyar dan ɗan’adam (wato psychology), wanda ya tabbatar da cewa hassada tana jefa mutum cikin damuwa da ciwon zuciya.

Yadda Hassada Take Hana Jin Daɗi:

Hassada tana hana mai hassada jin daɗi ta fuskoki masu yawa da suka haɗa da:

● Mai hassada yana rayuwa cikin baƙin ciki, saboda yana kallon wasu yana jin haushinsu.
Yana cike da damuwa, saboda yana son a cire wa wani wata ni’ima a maimakon ya mai da hankali kan kansa.
● Mai hassada yana ƙin farin cikin wasu, idan wani ya yi nasara, sai ya ji haushi a maimakon ya taya su murna.

Ga Wa su Misali a Rayuwa:
1. Idan mutum yana jin haushin wani saboda ya sami aiki, yana iya shafe kwanaki yana tunanin hakan a maimakon neman na kansa.
2. Idan mutum yana jin haushin abokin karatunsa saboda ya fi shi kyau, yana iya jin ƙunci da matsin lamba a maimakon ƙoƙarin kyautata halinsa. Allah Ya tsare mu daga hassada, Ya sa mu kasance cikin masu gode Masa da kyawawan halaye! Amin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]
  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  • An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
  • GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa
  • ’Yan daba sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna
  • ’Yan bindiga sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kai Tsakanin Iraniyawa Saboda Amfanin Kasar
  • Dubban Mutane Sun Fito Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Kama Magajin Garin Istambul
  • An Bukaci Gwamnati A Kowani Mataki Da Ta Taimakawa Yaki Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Gobara Ta Babbake Wani Shago A Jihar Kwara