Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu
Published: 14th, February 2025 GMT
Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96.
Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar.
Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa“Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96.
Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya gaba ɗaya.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannu a madadin iyalan Madam Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Madam Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo), da Mista Obafemi Ayo-Adebanjo.
Shahararren Lauya, tsohon sakataren Ƙungiyar Action Group kuma shugaban Ƙungiyar Afenifere na Ƙasa, Adebanjo ya rasu ya bar matarsa, Cif Christy Ayo-Adebanjo da ’ya’ya, jikoki da ’ya’yan jikoki.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Matasan Jihar Jigawa Sun Karrama Gwamna Umar Namadi
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu.
A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da J-Teach, da J-Agro, da J-Health, da J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya.
A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna godiya bisa kokarinsa na ci gaban matasa tare da sharbar romon dimokradiyya.
A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya nuna matukar farin cikinsa da wannan karramawar da matasan suka yi masa.
Yana mai cewar wannan girmamawar ba tasa ce kadai ba, ta daukacin al’ummar Jihar Jigawa ce gaba daya ba shi kadai ba.
A don haka, ya yaba wa matasan bisa jajircewarsu wajen kafa kyakkyawar rayuwa nan gaba, da kuma taimakawa ci gaban al’umma.
Malam Umar Namadi, ya yi nuni da cewar, matasan Jigawa sun nuna kwarewa da kishin kasa wajen tabbatar da ci gaban jihar.
Yana mai cewar, shakka babu, da irin wannan himma da kwazon matasa, jihar za ta ci gaba da samun ci gaba a fannoni da dama.
Sai dai kuma, Namadi ya bukaci matasan da su ci gaba da kokari wajen bunkasa jihar, yana mai jaddada cewar ci gaban Jigawa na hannun al’ummarta.
Ya kuma tabbatar da kudirin gwamnatinsa na kara samar da damarmaki ga matasa, ta hanyar daukar aiki, da kuma bunkasa tattalin arziki, domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga jihar.
Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin da Sakataren Gwamnatin, Malam Bala Ibrahim da kwamishinoni da sauran jami’an gwamnatin Jihar.
Usman Mohammed Zaria