Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU
Published: 14th, February 2025 GMT
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia domin halartar zaman taro karo na 38 na shugabannin ƙasashen ƙungiyar Afirka ta AU.
Shugaban wanda ya sauka a birnin Addis Ababa a daren ranar Alhamis ya samu tarba daga mataimakin shugaban kula da harkokin ƙasar Ethiopian, Eshetu Legesse da ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar da kuma mai kula da ofishin jakadancin Najeriya da ke Ethiopian, Ambasada Nasir Aminu.
Daga baya Ambasada Tuggar ya yi wa shugaba Tinubu bayani kan taron da kuma wasu nasarorin diflomasiyya da ƙasar ta samu, zaman da ya kai har misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren Juma’a.
Daga cikin nasarorin har da sake zaɓen Ambasada Bankole Adeoye a matsayin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na AU.
Har ila yau Najeriya ta ci gaba da zama a kwamitin zaman lafiya da tsaro na Ƙungiyar Afirka, yana mai jaddada, a cikin kalaman Ambasada Tuggar, “Jagorancin Najeriya da jajircewarta kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar”.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.
Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.
Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.