Aminiya:
2025-03-24@22:47:58 GMT

Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano

Published: 14th, February 2025 GMT

Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48.

Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Hotoro.

Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano

A cewar Hukumar FRSC, haɗarin ya rutsa da wata motar tirela ƙirar DAF ɗauke da kayayyaki da fasinjoji. Bincike na farko ya nuna cewa direban ya yi tuƙin ganganci saboda gudu wanda hakan ya sa motar ta kauce hanya ta afka ƙarƙashin gadar.

Rahotanni sun nuna cewa, adadin waɗanda haɗarin ya rutsa da su ya kai 71, mutum 48 ne suka jikkata, yayin da 23 suka mutu.

Jami’an bayar da agajin gaggawa na Hukumar FRSC tare da haɗin gwiwar rundunar ’yan sandan Najeriya, sun isa wurin cikin gaggawa domin gudanar da aikin ceto tare da dawo da zirga-zirgar ababen hawa.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed domin kula da lafiyarsu cikin gaggawa.

Bayan faruwar haɗarin, Kwamandan hukumar FRSC reshen Kano, CC UM Matazu, ya tura jami’an bincike domin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin haɗarin.

Ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hadarin tirela

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya

Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya.

A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina.

Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci

Bayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi.

Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe

Sauran fitattun ’yan siyasar da suka ziyarci Gwamna Radda sun haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Mu’azu.

Akwai kuma fitaccen attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal da kuma tauraron tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa da su ma suka jajanta wa gwamnan a kan rashin.

Dukkansu sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya jiƙan Hajiya Safara’u Ya sa ta huta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matasa Sun Daka Wawasu Kan Tirelar Kayan Agajin Ramadan Na Seyi Tinubu A Gombe 
  • NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano
  • Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi
  • Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
  • An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano
  • Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa
  • An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar
  • Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
  • Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba