USAID na ɗaukar nauyin Boko Haram —Dan Majalisar Amurka
Published: 14th, February 2025 GMT
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis.
Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula.
Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin.
A yayin zaman wanda ya mayar da hankali kan zargin karkatar da kudaden, Perry ya ce kuɗaɗen masu biyan haraji, “Dala miliyan 697 a duk shekara USAID krnkashewa, da kuma safarar kudaden kudade kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda da Boko Haram da ISIS Khorasan, da kuma sansanonin horar da ’yan ta’adda.”
Ya kuma ce hukumar ta USAID ta bayar da dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, inda ya yi zargin wata shaida ko da ke nuna gina makarantun.
Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin rufe hukumar ta USAID, kan zargin ta da cin hanci da rashawa a wani sako da ya wallafa.
Shi ma Elon Musk, abokin Trump, kuma shugaban ma’aikatar kula da ayyukan gwamnati, ya soki hukumar ta USAID, yana mai zargin cewa tana gudanar da ayyukan damfara.
Daga cikin wasu sukar, Musk ya yi iƙirarin cewa USAID tana “aikin leƙen asiri kamar CIA” har ma da “binciken kuɗaɗen binciken makaman ƙare-dangi, gami da COVID-19, wanda ya kashe miliyoyin mutane.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidan Shugaban Kasa Ta Ba Matan Arewa Ta Gabas Su Dubu Tallafin Naira Miliyan 50
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar.
Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar.
Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis da tsakar rana, ta samu tarba daga gwamna Agbu Kefas da matarsa, Misis Agyin Kefas tare da manyan jami’an gwamnati, da kuma dimbin magoya bayan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar da kuma babbar jam’iyyar adawa ta APC.
Mrs Tinubu ta kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Taraba, tare da rakiyar uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Ali Pate, da babban daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko na kasa Dr Muyi Aina da dai sauransu.
Ziyarar ta na kuma da nufin karfafa gwiwar ma’aikatan kiwon lafiya na sahun gaba ta hanyar ba da tallafi da kuma sanin irin kokarin da suke yi, da kuma wayar da kan jama’a game da cutar kanjamau, musamman yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa ’ya’ya.
Da take jawabi a yayin ganawarta da shugabannin gargajiya, Sen. Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa hada kai da sarakunan gargajiya zai taimaka wa gwamnatin tarayya wajen isar da sako game da samarwa da kuma maganin cutar kanjamau da tarin fuka kyauta, inda ta bayyana muhimmiyar rawar da suke takawa wajen hada kan jama’a.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba kuma Aku Uka na Wukari, HRM Manu Ishaku Adda Ali, ya bayyana ziyarar Misis Tinubu a matsayin alheri ga jihar.
Sai dai Sanata Oluremi Tinubu, jim kadan bayan ganawarta da shugabannin gargajiya, ta zarce zuwa filin wasa na Jolly Nyame, inda ta kaddamar da rabon kayayyakin sana’o’in ga ungozoma a fadin yankin Arewa maso Gabas.
A nata jawabin, ta kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan kiwon lafiya da nufin rage mace-macen mata da kananan yara a fadin kasar nan.
A nasa jawabin, Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ya ce a yankin Arewa maso Gabas kadai, an horar da ma’aikatan kiwon lafiya 8,500, daga cikinsu 1,300 daga jihar Taraba.
A cewarsa, sama da cibiyoyin kiwon lafiya 1,000 ne ke samun tallafi a duk shekara daga asusun samar da kiwon lafiyai, ciki har da 170 a jihar.
Gwamna Agbu Kefas ya yabawa uwargidan shugaban kasar bisa wannan karimcin, inda ya ce jihar ta yi tarayya cikin hangen nesa na shirin sabunta fata.
A nata bangaren, uwargidan gwamnan, Misis Agyin Kefas, ita ma ta nuna jin dadin ta bisa yadda aka yi musu dauki, sannan ta yabawa ministan lafiya da walwalar jama’a bisa jajircewar sa.
A halin da ake ciki, Sanata Oluremi Tinubu ya mika kayan sana’o’in hannu guda 10,000 ga ungozoma a fadin jihohin Arewa maso Gabas shida, sannan ta mika chekin kudi naira miliyan 50 domin tallafa wa mata 1,000 a jihar Taraba.
Sani Sulaiman