Sin Ba Za Ta Shiga Gasar Makamai Da Sauran Kasashen Duniya Ba
Published: 14th, February 2025 GMT
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya.
Game da hadin gwiwar Sin da Rasha, Guo Jiakun ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu bai shafi wani bangare na uku ba, kuma wani karin bangare ba zai yi tasiri kan hadin gwiwar ba.
Bugu da kari, game da batun Amurka za ta kara tallafin aikin soja ga Indiya tun daga shekarar bana, Guo Jiakun ya ce, bai kamata a yi amfani da kasar Sin don bunkasa dangantaka da kuma gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ba, kuma kada a tayar da siyasar kungiya da kuma yaki tsakanin sassa daban daban.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yamen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Tashar Jiragen Sama Na Bengerion A HKI
Sojojin kasar Yeman sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tashar jiragen sama ta Bengerion a birnin Tel’aviv na HKI a daren jiya laraba don tallafawa falasdinawa a gaza wadanda sojojin HKI suke kashewa bayan yi masu kofar rago ta shigo da abinci da abinsha cikin yankin na kimani wata guda.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgedia Janar Yahya Saree, kakakin sojojin kasar na fadar haka a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa sojojin sun yi amfani da makami mai linzami samfurin Falasdin-2 mai saurin fiye da saurin sauti, wato Hypersonic don kai wannan harin.
Tashar jiragen sama mafi girma a HKI dai ita ce ta Bengerion dake tazarar kilomita 20 daga birnin Tel’aviv. Saree ya kara da cewa makamin ya fada kan inda aka nufa da shi a tashar tare da nasara.
A wani labarin kuma sojojin kasar ta Yemen sun bada labarin kakkabo jirin leken asiri da kuma yaki na kasar Amurka wanda ake kira MQ-9 a sararin samaniyar kasar Yemen , kuma shi ne 20 da suka sauke tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a cikin watan Octoban shekara ta 2023.
Har’ila yau tun ranar Abasar da ta gabata ne sojojin kasar ta Yemen suna maida martani kan sojojin Amurka da suke tekun red sea da irin wadannan makamai.