Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Hadu Da Fushin ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa
Published: 14th, February 2025 GMT
‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka kaddamar da munanan hare-hare a kan sansanin Jenin sannan wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden bama-bamai kan gidajen Falasdinawa.
A halin da ake ciki kuma, Bataliyar Nablus da ke karkashin Sarayal-Quds na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa sojojin mamayar Isra’ila hari da harsasai da tada bama-bamai, yayin da dakarun shahidan Al-Aqsa suka tabbatar da gwabza kazamin fada da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin mamayar Isra ila da sojojin mamayar
এছাড়াও পড়ুন:
A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata.
Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa mazauna yankunan Sultan, Karama, da Awda da ke arewacin zirin Gaza, inda suka bukace su da su bar gidajensu, su koma zuwa yankunan kudancin Gaza.
Majiyoyin cikin gida sun ba da rahoton cewa, an kai wasu wadanda suka samu raunuka da dama da suka hada da wanda ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza.