Limamin Juma’ar Birnin Tehran Ya Ce; Al’ummar Iran Sun Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka
Published: 14th, February 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani da kakkausar murya ga kalamai da kuma matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ta hanyar halartar gagarumar zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran.
Ayatullah Khatami ya kara da cewa: A yau daga mimbarin Juma’a da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yana tabbatar da cewa: Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci wannan zanga-zangar tare da jaddada sha’awa, kuma irin wannan zanga-zanga ta bana ta fi ta kowace shekara daraja. Limamin Juma’ar ya jaddada cewa: Makiya suna magana ne a kan wuce gona da iri da bama-bamai, don haka ya ce: Trump mahaukaci ne wanda yake dauke da nazarin cewa; Ku gabatar da mu ta hanyar da za su tsorata; Ya kara da cewa: Ku gaya wa mutane cewa yatsarmu tana kan hanya, kuma idan kun yi rashin biyayya, za mu kai muku hari, Sayyid Khatami ya kara da cewa: Hakika al’ummar Iran suna daukar Trump a matsayin mahaukaci ne, kuma zasu kara masa hauka da yardan Allah Madaukaki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
Sojojin Sudan sun sanar a yau Juma’a cewa sun kwace iko da fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Khartum, bayan da su ka kori mayakan rundunar kai daukin gaggawa.
Majiyar ta ce, sojojin na Sudan sun fara da kutsawa cikin fadar shugaban kasar ne, ta mashigar gabas,bayan da su ka kashe mayakan rundunar kai daukin gaggawa da dama,yayin da wasu da dama su ka gudu zuwa cikin kasuwar dake kusa.
Bayanin da sojojin na Sudan su ka fitar ya kunshi cewa; Mun murkushe mayakan Duqlu, ‘yan ta’adda a tsakiyar birnin Khartum da kuma kasuwar Larabawa da ginin fadar shugaban kasa da sauran ma’aikatu.”
Har ila yau majiyar sojan na Sudan ta ce,su kuma yi nasarar rusa makamai da motocin yakin rundunar kai daukin ggagawar,kamar kuma yadda ta kame wasu masu maya.
Janar Nabil Abdullah wanda shi ne kakakin sojan na Sudan ya sanar da cewa; Za su ci gaba kai hare-hare a cikin dukkanin fagagen yaki har samun nasara.