CBN Ya Sahale Wa Masu Musayar Kudade Sayen Dala 25,000 A Mako
Published: 14th, February 2025 GMT
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin.
Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar kudaden, za su iya chazar masu sayen kudaden.
“Dole ne dilolin da su gabatar da rahotannin su ga sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, na kudaden da suka sayar ga masu hada-hadar musayar kudaden, inda su kuma masu hada-hadar musayar kudaden, dole ne su rinka gabatar da ribar da suka samu a kullum ta saye da sayar kudaden, ta hanyar amfani da tsarin cibiyoyin hada-hadar kudade, wato FIFd.” In ji CBN.
কীওয়ার্ড: sayar kudaden
এছাড়াও পড়ুন:
‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025.
Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis.
Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a BornoYa sanar da masu yi wa ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da Hukumar NYSC cewa an shirya kuɗaɗen alawus ɗin don fara biya.
Ya bayyana cewa jinkirin aiwatar da sabon alawus ɗin ya biyo bayan rattaba hannu ne kan kasafin kuɗi na shekarar 2025.
Yayin da yake yabawa mambobin NYSC bisa kiyaye manufofin shugabannin da suka kafa NYSC ta hanyar samar da haɗin kan ƙasa, haɗe kai da ci gaban ƙasa, shugaban NYSC ya roƙe su da su yi amfani da ma’anar yadda aka rubuta taken waƙen NYSC.