Bidiyon TikTok: Jami’ar UNIZIK ta kori ɗalibar da ta ci kwalar malami
Published: 14th, February 2025 GMT
Hukumomin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (Unizik) da ke, Awka a Jihar Anambra ta kori ɗalibar nan mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cin kwalar wani malamin jami’ar Dakta Chukwudi Okoye.
A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga Goddy-Mbakwe ta far wa malamin jami’ar, Dakta Chukwudi bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani wuri da ke harabar jami’ar.
A cikin takardar korar ɗalibar da jami’ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wanda muƙaddashin magatakardar jami’ar, Ɓictor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin korar ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami’ar ta yi.
Hukumar jami’ar ta ce ”Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami’ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)”, in ji takardar korar.
Bidiyon cin kwalar malamin ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta kiraye-kirayen ɗaukar mataki kan lamarin.
Hukumar Jami’ar ta buƙaci ɗalibar da ta gaggauta ficewa daga harabar jami’ar tare da mayar wa jami’ar duk wasu abubuwan da ke hannun ɗalibar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗalibar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Amurka Yace Yana Kokarin cimma yarjeniya da kasar China Dangane da Tiktok
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa yana kokarin cimma matsaya da kasar Chaina dangane da kamfanin sadarwa da kuma yanar gizo na TIK Tok.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na ‘Trump Social,
Labarin ya kara da cewa shugaban yana fadar haka a dai dai lokacinda gwamnatin Amurka ta dorawa kayakin kasar China masu shigowa Amurka kudin fito na kasha 125%.
Tun zagaye na farko na shugabancinsa ne shugaban ya fara rigima da kamfanin Tiktok na kasar China wanda ya sami karbuwa a cikin Amurka da kuma kasashen duniya da dama. Amurka tana ganin shafin yanar gizo na tiktok barzane ce ga tsaron kasar Amurka. Kuma har ta bukaci kasashe kawayenta a duniya su daina mafani da Tiktok.
A zangon shugabancinsa na farko dai shugaban ya haramta wayar tafi da gidanka mafi girma a kasar Chaina wato hawawi da kuma kamfanin internet na G%. wadanda yake ganin barazana ne da tsaro da kuma bangaren tattalin arziki ga kasar ta Amurka.