Gobara ta ƙone ofishin zaɓe INEC a Sakkwato
Published: 14th, February 2025 GMT
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki.
Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa.
A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin jihar, Hauwa Aliyu Kangiwa ta ruwaito.
Ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata 11 ga watan Fabrairun 2025.
“Duk ginin ofishin ya lalace. Kayayyakin da suka lalace sun haɗa da tebura da kujeru da kayan aiki da kayan zaɓe da ake iya ɗauka, daga cikinsu akwai akwatunan zaɓe 558, rumfar kaɗa ƙuri’a 186, jakunkuna 186 na zaɓe da kuma kayayyakin da suka haɗa da manyan tankunan ruwa guda 12 (litta 1,000), tabarmin barci 400 da bokitan robobi 300.
“Rahoto na farko daga ofishinmu na jihar ya nuna cewa an samu ƙaruwar wutar lantarki kafin faruwar lamarin,” in ji Olumekun.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympic
‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic.
An zabi Kirsty ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris.
Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic.
Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach dan kasar Jamus.