Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53.

Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.

1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Ayyuka 8 A Goman Karshe na Ramadan

A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:

Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan ibada, musamman a dararen mara a goman karshen watan Ramadan. Sallah: Musamman Sallar Tarawihi da Tahajjud, baya ga yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma yin nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin na farilla. Karatun Al-Kur’ani: A dage a yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi, a daren Lailatul Kadar, cikin kwana goman karshe. Addu’o’i: A dage da addu’o’in neman garafa da rahamar Allah da aljannah da kuma dacewa da alherin duniya da lahira da kuma neman tsari daga wuta da kuma sharrin duniya da na lahira. Mutum na iya yin addu’a a lokutan da ake amsa addu’o’i kamar lokacin Sahur ko bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin da cikin sujada ko a cikin sulusin karshe da dare da sauransu. Umrah: Hadisi ya nuna wanda ya yi Umra a cikin goman karshe na Ramadan zai samu ladar yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW). Zakka: Ana so duk Musulmi mai hali ya fitar da Zakkar Kono ya ba wa mabukata. Magidanci da da da hali zai fitar da sa’i daya (Mudun Nabi hudu) na hatsi, haka kuma zai fitar wa iyalansa da duk wanda yake ciyarwa. Ana iya fitarwa a bayar daga ranar 28 ga Ramadan har zuwa lokacin tafiya masallacin idi ranar Karamar Sallah. Kabbarori: Ana yin kabbarori daga bayan faduwar ranar jajibirin Karamar Sallah, har zuwa lokacin da za a idar da sallar idin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
  • Trump Ya Bayyana Dalilin Rufe Gidan Rediyon Muryar Amurka
  • Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
  • Tunisiya : Kaïs Saïed, ya kori firaministansa Kamel Madouri
  • MAGGI: Girke-girken Ramadan masu kawo sauyi da zumunta
  • Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan
  • Manyan Ayyuka 8 A Goman Karshe na Ramadan
  • Xi Jinping Ya Yi Rangadi a Birnin Lijiang Na Lardin Yunnan
  • A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
  • Mutane Da Dama Ne Ake Jin Tsoron Sun Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Daukar Gas Ta Yi Bindiga A Kan Gadar Karu A Birnin Abuja