Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa.

Kuma, kamfanonin kasashen biyu sun samu sabon ci gaba a bangaren makamashin gas da man fetur.

Tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da asusun kasar Kazakhstan na Samruk Kayzana da kungiyar ‘yan kasuwar kasar ta Atamekeh a Astana hedkwatar kasar Kazakhstan, tare da gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin ‘yan kasuwar kasashen biyu da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa 8, wadanda ke shafar bangaren makamashin gas da man fetur da aikin noma da jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa da sauransu.(Amina Xu)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

 Jagora: Siyasar Kasar  Iran  Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har  yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a kai ga warware sub a,kamar dawo da kudaden Iran da aka zuba a Bankunan kasar daga Korea Ta Kudu.

A nashi gefen sarkin Katar ya jinjinawa matakan da Iran din take dauka na taimakawa raunana a duniya, da kuma al’ummar Falasdinu, kuma yadda ta kasance a tare da Falasdinawa wani abu ne da ba za taba mancewa da shi ba har abada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya
  •  Jagora: Siyasar Kasar  Iran  Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta
  • Kamfanonin Sin Masu Zaman Kansu Na Taka Rawar Gani Ga Bunkasuwar Tattalin Arzikin Duniya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Watsi Da Karin Shuruddan Gwamnatin ‘Yan Sayoniyya Kan Tsagaita Bude Wuta
  • Juyin-juya-halin Kyautata Muhalli: Rawar Da Kasar Sin Ke Takawa Wajen Samar Da Makoma Mai Kyau
  • Kasashen Rasha Da Amurka Sun Kuduri Anniyar Kawo Karshen Yaki A Ukraine
  • Daga Munich Zuwa Addis Ababa, Ci Gaban Kasashe Daban Daban Na Tabbata
  • Sarkin Qatar Zai Zayarci Tehran A Gobe Laraba
  • Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU