Iran Ta Sanar Da Samun Sakwanni Daga Mahukuntan Syria
Published: 15th, February 2025 GMT
Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun yi musayar sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye.
Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece cewa, Muna cikin shiri da tanadin sake dawo da alaka da kasar Syria anan gaba.
Har ila yau. Shaibani ya ce; Muna bin diddigin abubuwan da suke faruwa a Syria, kuma za mu dauki matsaya a lokacin da ya dace.”
Haka nan kuma ya ce; Muna kallon Syria ne a matsayin kasa wacce take da matsayi a cikin yankin yammacin Asiya, kuma mun yi imani da cewa, al’ummar kasar ne za su ayyana makomarta, don haka ya zama wajibi dukkanin bangarorin siyasar da ake da su a kasar su shiga ayi da su.”
Dangane da ziyarar da ya kai kasar Rasha, Shaibani ya ce; yana yin ziyarar ne domin tattaunawa da jami’i mai kula da harkokin Syria da kuma mataimakin ministan harkokin waje.
Shaibani ya kuma kara da cewa; kasashen Iran da Rasha suna da mastaya iri daya akan batutuwa mabanbanta da su ka shafi Syria,kuma a yayin wannan ziyarar sun cimma matsaya akan ci gaba da tattaunawa da yin shawarwari a tsakaninsu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shaibani ya
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Sanar Da Shahadar Wani Jagoranta Da HKI Ta Kashe A Lebanon
Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon.
Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a karkashin “Tufan-ak-Aksa” bayan da ‘yan mamayar HKI su ka yi masa kisan gilla a garin Saida dake kudancin Lebanon a jiya Litinin.
Har ila yau dakarun Kassam sun yi bayani akan rawar da shahidin ya taka a fagen gwgawarmaya da jihadi akan ‘yan mamaya, tun daga boren Intifada na Aksa, har zuwa farmakin guguwar Aksa.
Haka nan kuma bayanin na Kassam ya ce, Abul-Baraa ya riski dan’uwansa Shahin Hamzah Shahid wanda ya gabace shi da yin shahada da kuma sauran ‘yan’uwansa shahidai masu tsarki.
Kassam din ta yi alkawalin ci gaba da tafiya akan tafarkin shahidin na jihadi da gwagwarmaya har zuwa cimma manufofin al’ummar Falasdinu na ‘yanto da Falasdinu da fursunonin da suke kurkuku da kuma komawar Falasdinawa ‘yan hijira zuwa gida.