Gwamnan Zamfara Ya Mika Sansanin Karbar Tubabbun ‘Yan Bindiga Ga Sojan Nijeriya
Published: 15th, February 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.
Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su.
Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.
A cewarsa, shirin ya yi koyi ne da shirin ‘Operation Safe Corridor’ a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar kawar da tsaffin mayakan na Boko Haram tare da dawo da su cikin al’umma.
“Amma ga wadanda suka yi niyyar mika makamansu ba tare da wani sharadi ba suna da ‘yancin yin hakan.
Da yake jaddada cewa, kafa hedkwatar tsaro ta Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma zai bada damar kwance damara, da wargazawa, da kuma cudanya da tubabbun ‘yan fashi a cikin al’umma.
Ya kuma mika godiyarsa ga babban hafsan hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa bisa ganin jihar Zamfara ta cancanci karbar bakuncin rundunar Operation Safe Corridor na 3 a kasar nan.
“Ina kuma so in gode wa shugaban kwamitin aiwatar da ayyukan Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma, Manjo Janar EV Onumajoro, wanda kuma shi ne babban hafsan tsaro na hedikwatar tsaron Najeriya, da tawagarsa saboda ganin Zamfara ta dace da kafa hedkwatar wannan muhimmin sashi.
Tun da farko, Manjo Janar Onumajuru, wanda ya wakilci babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, ya yabawa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa sojoji a yakin da ake da ‘yan bindiga a Zamfara.
Bayan karbar ragamar wannan sansanin, za mu ci gaba da hada kai da mai girma Gwamna da al’ummar Zamfara, wadanda su ne masu ruwa da tsaki a wannan aiki, domin tabbatar da hadin kai don kwalliya ta biyan kudin sabulu.
AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tsaro Zamfara Arewa maso Yamma
এছাড়াও পড়ুন:
Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo
A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar.
Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas.
Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG.
Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar.
A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka tsara rufe rumfunan zaben.
Za a iya fara sanar da sakamakon zaben daga gobe Lahadi.