Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai A Yankin Baluchestan Na Pakistan
Published: 15th, February 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.
A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar su ka yi wa ma’aikatan hako ma’adanai dake yankin Harnai a arewacin gundumar ta Baluchestan.
Haka nan kuma ya ce, a duk inda ayyukan ta’addanci suke faruwa jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin Allawadai da shi.
Jami’in diplomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar ganin an kara samar da hadin kai a tsakanin Iran da kasar ta Pakistan a fagen fada da ayyukan ta’addanci.
A jiya Juma’a ne dai wani bom ya tashi da wata mota wacce take dauke da ma’aikatan hako ma’adanai a shahrag dake yankin Harnai.
Jami’an ‘yan sandan yankin na Baluchestan sun sanar da cewa ma’aikatar hako ma’adanai 11 ne su ka kwanta dama, yayin da wani adadi mai yawa nasu ya jikkata.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai wannan harin.
Sai dai a baya kungiyar nan ta ‘yan awaren yankin na Baluchestan mai suna Baluch Liberation Army ta rika daukar alhakin hare-hare irin wadannan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojojin Qassam Ta Tabbatar Da Kashe Wani Jami’anta A Lebanon
Bangaren kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ya tabbatar da shahadar wani daga cikin jami’in kungiyar a wani harin Isra’ila.
Muhammad Ibrahim Shaheen, ya yi shahada ne a wani harin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai a Sidon.
Kassam Brigades ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi tsayin daka kan zalincin Isra’ila, ciki har da lokacin yakin Gaza.
Ita ma Isra’ila ta tabbatar da kashe jami’in na Hamas a harin da ta ce ta kai kan a Lebanon
Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin ta sama a Sidon, inda suka ce sun kashe wani “dan ta’adda” Bafalasdine.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kokarin ganin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Isra’ila da Hamas ta daure.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya fada jiya Lahadi cewa, tawagar tattaunawa ta kasar za ta je birnin Alkahira domin tattaunawa kan aiwatar da yarjejeniyar.
Sanarwar ta kara da cewa, da farko dai tawagar za ta fara tattaunawa ce kan ci gaba da aiwatar da mataki na daya na yarjejeniyar tsagaita wutar, kana za a ba ta umarni a kan ci gaba da tattaunawa game da kashi na biyu, bayan taron majalisar tsaron Isra’ila.