Abu Ubaidah: Hamas Za Ta Saki Fursunoni 3 A Yau Asabar
Published: 15th, February 2025 GMT
Kakakin dakarun rundunar “Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa za su saki fursunoni 3 na “Isra’ilawa” a wannan rana ta Asabar.
A jiya Juma’a ne dai kakakin na dakarun rundunar “ Kassam” ya fitar da sanarwar cewa za saki fursunoni uku da suke rike da su da su ne: Shasha Alexander,Sagi Dikel Hen,Yaei Horun
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun dakarun na “Kassam” Abu Ubaidah ta sanar da dakatar da duk wani batu na cigaba das akin fursunonin sai illa masha Allahu.
Sai dai daga ranar Alhamis zuwa jiya Juma’a masu shiga tsakani da su ne kasashen Katar da Masar, sun yi kokarin gusar da matsalar da ta kunno kai daga gefen HKI da hakan ya bayar da damar sake komawa kan batun musayar fursunonin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
IRGC: Za Mu Kai Farmakin “ Wa’adus-Sadik” Na 3 Akan ‘Yan Mamaya
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3” a lokacin da ya dace.
Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba su cimma manufarsu ba.
Iran dai ta kai wa HKI hare-hare guda biyu a aka bai wa Sunan “ Wa’adussadik” na daya da na biyu. Hare-haren na Iran dai sun kasance mayar da martani ne akan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Syria da kuma kashe mata jami’an soja masu bayar da shawara ga gwamnatin Damascuss. Na biyun kuwa ya kasance mayar da martani akan kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka kawo a Tehran wanda ya yi sanadiyyar shahadar shugaban kungiyar Hamas Shahid Isma’ila Haniyyah.
A wani gefen, shugaban kungiyar Hamas a yankin Gaza, Khalil Hayyah ya fada a makon da ya shude cewa; Iran ta kasance a sahun gaba wajen taimakawa gwgawarmayar Falasdinu, kuma muna da tabbacin cewa za ta cigaba da yin hakan.