‘Yan Majalisar Najeriya Sun Amince Da Karin Dala Miliyan 200 A Cikin Kasafin Kudin 2025
Published: 15th, February 2025 GMT
Amincewa da Karin kudin dai ya zo ne domin cike gibin da aka samu, bayan da Amurka ta yanke kudaden taimakon da take bayarwa a fagen kiwon lafiya.
A shekarar 2023 Kasar Najeriya mai mutane fiye da miliyan 200 tana cikin 10 na farko da su ka fi karbar tallafin hukumar Amurka na raya kasashe ( USAID). Sai dai a halin yanzu shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dakatar da wannan taimakon na tsawon kwanaki 90.
Wani dan majalisar dattijan Najeriya Sen. Adeola Olamkilekan wanda ya yi Magana a yayin zaman majalisar na amincewa da Karin kasafin kudin ya ce; Kasar ta za ji jiki sosai saboda yadda Amurka ta yanke tallafin, musamman a fagen dakile cutuka.
Dala miliyan 200 da aka amince da su, suna cikin kasafin kudin kasar ne na dala biliyan 36.6.
Za a yi amfani da mafi yawancin kudaden ne dai domin samar da magungunan riga-kafi da kuma magance cututtuka na annoba.
A shekarar 2023 Amerika ta bai wa Najeirya dala miliyan 600, domin amfani da su a fagen kiwon lafiya. Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce, an bayar da wadancan kudaden ne dai domin riga-kafin zazzabin Malariya, da kuma rika-kafin cutar HIV da magungunanta.
Bugu da kari, yanke taimakon na Amurka zai iya shafar fagen ayyukan jin kai, musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar da ake fama da matsalar masu dauke da makamai dake kashe mutane tun 2009 da ya haddasa kwararar ‘yan gudun hijira masu yawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma da ke lardin Al-Bayda a jiya Asabar .
Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin yankunan Kitif da kuma Al-Bogee daga cikin lardin Sa’ada.
Labarin ya kara da cewa wannan yankin yana daga cikin yankunan da ake fafatawa da sojojin Amurka, kuma suna yawaita kan hare-hare a cikinsa.