Kissoshin Rayuwa : Immam Hassan Dan Ali (a) 17
Published: 15th, February 2025 GMT
17-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen, Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga Fitima(s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar yadda al-amura suka kasance bayan wafatin manzon All..(s) a madina musamman a masallacin manzon All..(s), inda Khalifa Umar ya hana mutanen fadar cewa manzon All..(s) ya rasu. Kuma har ya kai ga yana masu barazanan zai bugesu da takubin da ke hannunsa.
Sannan mun ji yadda ya sawya sama da kasa, a lokacinda Abubakar ya zo masallacin, ya fadawa mutane a cikin masallacin manzon All..(s) kan cewa manzon All..(s) ya rasu.
Bayan haka, sai suka je Sakifa inda Ansar suke taro, a asirce a tsakaninsu don zaben Sa’adu dan Ubada, a matsayin Khalifa, har’ila yau munji yadda aka kashe Sa’adu dan Ubada din a shekara ta 14 ko15 bayan hijira, amma wadanda suka kashe shi, suka ce, ai aljana ce ta kashe shi, da kibiyoyi biyu a kan kirginsa, kuma suka jefa gawarsa a cikin rijiya.
Sannan munji mai yu wa dalilan da suka sa Ansar sun so su zabi Sa’adu a matsayin Khalifa bayan wafatin manzon All..(s). ba tare da sun shawarci iyalan gidan manzon All..(s) ba. Mun ce mai yuwa suna sun kiyaye mutuncinsu da matsayinsu idan wasu ba iyalan gidan manzon All…ba suka karbi shugabancin al-umma.
Daga karshen mun yi maganar cewa shirin kauda iyalan gidan manzon All..(s) daga matsayin da All..da manzonsa (s) suka basu, an dade da kulla shi, saboda manzon All..Ya sha fadawa Aliyu(a) kan cewa akwai wadanda suke adawa da shi a cikin sahabbansa, amma baza su bayyana masa hakan ba, sai bayan wafatinsa.
Sannan munji cewa shugabannnin juyin mulkin da aka yiwa Amirulmuminin (a) bayan wafatin manzon All..(s), manya manyan kuraishawa ne wadanda Abubakar da Umar tare da taimakon yayansu, kuma matan manzon All..(s) suka shirya, saboda dalilan da muka bayyana.
Har’ila yau idan mun koma kan Ansar, wadanda suka taru a Sakifa don gabatar da Sa’adu dan Ubada a matsayin Khalifa. Zamu ga mcewa, shi Sa’adu, ya na da wadanda suke takara da shi, hatta a cikin Ansar kansu. Da farko akwai dan Amminsa wanda ake kira Bashir dan Sa’ad dan Ubada dan Thaalaba Alhazraji, sai kuma Usaid bin Hudair shugaban kabilar Aus cikin Ansar, suna takara da shi a wannan matsayin da yak enema. Ko kuma suna hasadar sa a kan wannan matsayin, ko wanne daga cikinsu ya na ganin ya cancanci matsayin.
Hakama Uwaim dan Sa’ida al-awsi da kuma da Mu’in dan Adiyyi, abokin kungiyar Abubakar ne, duk da cewa su ma Ansar ne.
Suna abota da shi a rayuwar manzon All..(s). don haka wadannan mutane biyu basa son Sa’adu dan Ubada, ya zama Khalifa, don haka sai suka yi sauri suka je suka fadawa Abubakar kan cewa Ansar, sun gabatar da Sa’adu dan Ubada, zasu yi masa mubaya’a a Sakifa.
A lokacinne Abubakar da Umar da Abu ubaida dan jarra da kuma salam maula Abu Khuzaifa suka sami wannan labarin, sun yi gaggawa suka je Sakifa, sannan abinda ya faru ya faru, har aka yiwa Abubakar Bai’a.
Kafin bai’ar dai, Umar yana son yayi magana, amma ya na magana da fushi, sai Abubakar ya ce masa ya yi shiru, shi zai fara magana.
Sai ya ce:
Mu musu hijira mune wadanda suka rika kowa shiga musulunci. Kuma mun fi kowa nasaba mai kyau, kuma mun fito ne daga gidaje masu Daraja a cikin Kuraishawa, …. Sannan mun fi su kusanci ga manzon All..(s).
Ku ‘yan’uwammu ne, a addinin musulunci, ku masu tarayya da mu ne a cikin wannan addinin,
Kun taimawa masu hijira, kun kuma kun yelwata mana, All..ya saka maku da Alkhairi. Don haka mune shuwagabanni ku kuma wazirai, wato mataimaka.
Larabawa ba za bi, wani a cikin wannan addini ba sai. wanda ya kasance daga wannan kabilar, wato (kuraishawa).
Kada ku yi jayayya da yan uwanku musu hijira, a kan wannan matsayin, wanda All..ya fafitasu da shi.
Don haka na yarje maku, ku yi mubaya’a ga daya daga cikin wadannan mutane biyu (ya na Umar Dan Khaddabi, da Abu ubaida dan Jarrah). Karshen maganarsa Kenan.
Don haka idan mun dubi Khudunar Abubkar za mu fitar da dalilan da ya kawo na cancantar Kuraishawa ko Muhajirun da khalifanci.
01-Su ne na farkon musulunta.
02-Su ne dangin manzon All..(s) mafi kusa da shi.
Da farko bai yi Karin bayani a kan dalilansa na farko da na biyu ba.
Na cewa su suka fara Imani da manzon All..(s) ba .
Saboda farkon wanda ya yi Imani, ya karbi kiran manzon All..(s), ya kasance tare da shi a yakar makiyansa, ya kuma kare shi daga sharrin shuwagabannin Kuraishwa, kuma shi dan ammin manzon All..(s), kuma renonsa, sannan mijin diyarsa toli daya bari a duniya ne, mahaifin jikokin sa (s) biyu ne, kuma kofar ilmimsa ne, shi ne Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).
Abubakar ya yi watsi da duk wannan a cikin muhajirun, ko kuraishawa, idan ya na nufin kusanci ne ga manzon All…(s), wa ya fi Aliyu kusanci da shi.
A wasu baitocin da ya Aikawa Mu’awiya dan Abi Sufyan, a lokacinda ya aika masa wasika inda a ciki yake yabon kasa da cewa, ai shi ma kawun muminaine, wato manzon All…(s) ya auri Yarsa Uwar muminai “Ummu Habiba” don haka ita uwar muminaice to shi kuma ya zama Kawun muminai.
Sai Imam Ali (a) ya ba shi amsa da cewa:
Diyar manzon All..abokiyar zama ta ce (matata ce) Amariyarta ce. Tsokar jikinta ta garwaya da jini da kuma namar jikina.
Kuma Jikokin Ahmadu (s), Yaya nane daga wajenta. Wake da rabo irin rabona.?
Ga wanda yake da dukkan wadannan falaloli da kusanci da manzon All..Amma Abubakar ya manta da dukkan wadannan falaloli, ya gabatar da Abu ubaida dan Jarra da kuma Umar Dan Khaddabi, a matsayin khalifofin manzon All..(s) a cikin mujirun .
A wata jayayya da da su, Imam Ali (s) ya na fadawa Abubakar, “sun kawo hujja da itaciya sun bar yayanta”. Ya na nufin itaciya itace Kuraishawa, amma sun mata da yayan itaciyar wato, dangin manzon All..cikin Kuraishawa wato banu Hashim, da kuma zurriyar manzon All..(s) masu tsarki.
Ko menenen kusancinsu da manzon All..(s) ba su fi yayansa da jikokinsa da yayan amminsa kusa da shi.
A lokacin da manzon All..(s) ya yi wafati ya bar amminsa guda wato Abbas dan Abdul muttalib, amma shi bai dade da musulunta ba, manzon All..(s) ya yi wafati.
Bai dade a cikin addini ba, don ya mshiga addinin musulunci ne a fatahin Makka a shekarata 8 bayama hijira. Don haka a cikin Banu Hashim babu kamar Aliyu (a). Ya hada dukkan falalolin da suka bashi damar zama Khalifa.
*******************************************
Don haka Aliyu dan Abitalib shi ne shugaban Banu Hashim, dangin manzon All..(s) a lokacin.
Na farko wa ya Sanya Khalifa Abubakar wikilin Kuraishawa don zaben wanda zai shugabancesu?. Sannan idan har ya wakilce su, to akwai wanda ya fi wadanda ya gabatar a matsayin khalifofi a cikin kuraishawa, kuma sune ‘ya’yan manzon All..yayan amminsa(s).
Don haka Imam Ali (s) ya hujjacesu da abinda suka hujjace Ansar da shi a cikin wata kasidan da yi, yana cewa:
Idan da kusanci ne ka hujjace, mai husumarsu. To waninka ne yafi cancanta da al-amuran Annabi(s), ya kuma fika kusa. Idan da shura ce ka mallaki al-amuransu, to ta yaya haka zai kasance, wadanda suka cancanci bada shawara basa nan.A cikin wani khudubar sa dangane da wannan batun. yana cewa:…Wallahi ni dan’uwansa ne, (yana nufin Manzon All…(s), .. mai jibantar al-amarinsa ne, kuma dan’amminsa ne, kuma magajin ilminsa ne, wa ya cancanci gadonsa fiye da ni.
Hakika mutane sun ki bin Baban Alhasan, sun yi watsi da falalolinsa, da fifikonsa, da wasiyyan annabi (s) dangane da shi. Saboda kodayin shugabanci da khalifanci.
A lokacinda Abubakar ya kammala khudubarsa, wanda muka gabatar, ya kuma gabatar da Umar da Abu Ubaida dan Jarrah, a matsayin wadanda suka cancanci wannan matsayin a cikin Kuraishawa, ko muhajirun.
Sai Umar yayi sawri ya ce: Hakan zai kasance ka na da ranka (ya Abubakar)?, bai yu wa wani ya kawda kai daga matsayin da manzon All..(A) ya tsaida kai.
A nan sai mu ce: bamu san wani lokaci ne manzon All..(s) ya sanya shi Khalifansa ba!. Abinda muka sani shi ne, kwanaki kafin wafatin sa, manzon All..(s) ya sanya shi cikin rundunar da Usama yake jagoranta. Usama dan Zaidu, dan shekara 17 a duniya, inda manzon All..ya ce ya tafi kasar Roma ya kuma yaki kafirai a can.
Don haka manzon All..(s) ya bar shugaban Usama dan zaidu shugaban Abubakar da Umar ne. Shi ne kwamandan su a yakin.
A cikin wannan halin ne aka yiwa Abubakar Bai’a. Da farko Umar ne ya yi masa bai’a, sannan Bashir dan Ubada, dan uwan Sa’adu dan Ubada, sannan sauran wadanda suke cikin kungiyarsa wadanda suka hada da Usaid dan Hudair da Awim dan Sa’idah, da Mu’in dan Adiy, da Abu Ubaida dan Jarrah, da Salam maula abu Khuzaifa da Khalid dan walid, wanda ya fi kowa tsanantawa mutane, su yi bai’a wa Abubakar.
Banda haka Umar ya tilastawa wasu yin bai’a ga Abubakar, sannan a lokacinda mutane suke ribibin yi wa Abubakar Bai’a, sai wasunsu sun tattaka Sa’adu dan Ubada don yana kwance a kasa a lokacin saboda rashin lafiya.
Sai ansar suna cewa, an kashe Sa’adu, Sai Umar yace: Ku kashe shi, All..ya la’anci shi, shi ma’abucin fitina ne.
Bayan da aka yi masa Bai’a, sai mutanensa suka sa shi a gaba suna yabonsa suna masa kirari a matsayin Khalifan manzon All..(s), su na masa kamar yadda ake yi wa ‘Amarya’ zuwa gidan mijinta. suka raka shi zuwa masallacin manzon All..(s).
Sun yi haka ne. a lokacin gawar manzon All..(s) mai tsarki, tana kwance a kan gado ba’a kammala yi masa wanka ba da likkafani ba.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: iyalan gidan manzon All a matsayin Khalifa cikin Kuraishawa cikin kuraishawa wannan matsayin bayan wafatin wadanda suka masu sauraro wa Abubakar Abubakar ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Tituna Akan Kudi Naira Biliyan 6.3
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje.
Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin.
Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su.
Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran da zarar an kammala aikin zai bunkasa kasuwanci, da saukaka kalubalen sufuri, da bude sabbin hanyoyin tattalin arziki ga mazauna yankin.
Malam Umar Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar gina sabbin hanyoyi arba’in da bakwai na tsawon sama da kilomita dari tara a jihar.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka a dukkan hanyoyin da aka bayar da aikinsu.
A nasa jawabin kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Injiniya Gambo S Malam ya ce an bayar da aikin gina hanyar kanya Babba, zuwa Duzau zuwa Goron Maje akan kudi sama da naira biliyan shida.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Karamar Ministar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Babura ce ta kaddamar da aikin.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, mataimakin gwamnan jihar Jigawa Injiniya Aminu Usman, da kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim da dai sauransu.
Usman Muhammad Zaria