HausaTv:
2025-02-20@08:50:40 GMT

Kissoshin Rayuwa Imama Hassan (s) 18

Published: 15th, February 2025 GMT

18-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen, Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da na farko ga  Fitima(s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata mun yi Magana kan yadda Aka yiwa Abubakar bai’a a matsayin Khalifan manzon All..(s) a wani wuri da ake kira Sakifa.

Sannan mun bayyana cewa kafin haka Umar ya hana mutane su magana a kan wafatin manzon All..(s).  Ya kuma yi barazanar zai katse wuyar duk wanda ya yi hakan. Sannan mun bayya cewa ya yi haka ne, don saboda a lokacinda manzon All..(s) ya yi wafati, Abubakar baya cikin madina, yana wani wani wuna aki kira ‘Sarh’ a wajen madina.

Kuma bisa abinda wasu lamamai suke gani, yayi haka ne don kada wani ya fara maganar Khalifanci, sai Abubakar ya zo, don su aiwatar da shirinsu na juyin mulki wa Aliyu dan Abitalib (s).

Don haka ne da zaran Abubakar ya isa masallacin manzon All..(s), sai kome ya sauya. Suka shiga gidan manzon All..(s) tare, Abubakar ya daga mayafin da aka rufe fuskansa(s), ya ga fuskansa ya tabbatar da cewa. Da gaske ya yi wafati. Sai ya fita tare da shi Umar, zuwa msallacin manzon All..(s) ya yi khuduba ya na cewa:

‘Duk wanda yake bautawa Muhammadu, to Muhammadu(s) ya mutu, wanda kuma ya ke bautawa All..to lalle yana nan baya mutuwa. Sannan ya ja ayar Alkur’ani mai girma, wacce take tabbatar da hakan.

Daga nan sai labari ya zo masu kan cewa, Ansaru suna taro karkashin shugabancin Sa’adu dan Ubada, a sakifa. Sai suka yi gaggawa suka je. can suka shiga jayayya da Ansar kan wanda ya fi cancantar khalifanci. Abubakar ya yi Magana, a karshen maganarsa, ya yi nu ni ga Umar da Abu ubaida dan Jarrah, a matsayin wadanda suka cancanci khalifanci, a cikin muhajirun.

Sai Umar ya yi sauri ya ce, ai ba wanda ya fi cancatar wannan matsayin kamar shi matukar ya na da rai. Don haka Umar ne ya fara yi masa bai’a, sannan, sauran suka biyo.

Daga nan sai suka rakaci zuwa masallacin manzon All..(s) kamar yanda ake raka amarya zuwa dakin mijunta. Sannan munji wasu daga cikin martini da Imam Ali (a) ya yi masu dangane da wannan daga baya. Wato dangane da abinda ya faru a Sakifah. Da kuma cancantarsa da khalifancin manzon All..(s) fiye da kowa.

A lokacinda duk wadannan Al-amuran suke faruwa, Aliyu shagaltu da yi wa manzon All..(s) wanda ta likkafani ne, bai isa ya motsa ba, sai ya sa shi a makwancisa har zuwa ranar kiyama.

An yi wa khalifa Abubakar Bai’a da gaggawa a ranar da manzon All..(s) ya yi wafati.

Saurin da Khalifa Umar yake fada bayan da Abubakar ya mayar masa da Khalifincin, yana cewa

(Lalle bai’ar Abubakar ta kasance ba zata ce, All.. dai ya kiyaye musulmi sharrinta, duk wanda ya kira ku zuwa irinta nan gaba ku kashe shi).

Don haka malaman tarihi a duk tsawo tarihin musulunci sun yi ta bayani dangane da Kalmar (filtah), ko ba zata, menen manarta?, ba zata ne da gaske ne?, ko wani abu daban ne?.

Amma Umar ya soki bai’ar, saboda ba’a ginata kan asasi mai kyau da karfi ba. Ya kuma roki All..T ya kiyaye musulmi sharrinta.

A nan zamu dubu illolin bai’ar Abubakar a matsayin Khalifan manzon All..(s).

Aibin wannan bai’ar ita ce.

Da farko basu tuntubi iyalan gidan manzon All..ba a lokacinda suka kullata. Sannan yi watsi da wasiyyar manzon All..(s) dangane da hakan. Sun watsi da abin da ya fada masu, ya kuma nanata masu, kan cewa ya na barrin Alkur’ani da kuma iyalan gidansa a bayansa, kuma wanda ya rikesu zai tsira, wanda bai rike su tare ba, ya halaka.

Ko daa a ce babu wata aya, ko hadisi, babu Nissa kan Khalafincin iyalan gidan manzon All..(s), shin babu cancanci a jinkirta bai’ar ba har zuwa lokacinda za su kammala jana’izar manzon All..(s),?.

A matsayinsu na wadanda su ne mafi kusa da manzon All..(s), ?

Ga mijin diyarsa yana nan, Aliyu shugaan gidan manzon All..(s) bayansa bai kai matsayin da za’a tuntube shi ba, idan har bai kai ba, me yada Umar ya sa shi cikin kwamitin mutane 6 wadanda zasu zabi khalifa a tsakaninsu?. Wannan kawai yanan nuna cewa ya cancanci zama Khalifa tun lokacin wafatin manzon All..(s), ba sai bayan shekara 13 bayansa ba.

Iyalan gidansa sun fi kowa jin zafin wafatin manzon All..(s), an ce ana girmama mutum bayan wafatinsa ta zuriyyarsa da makusantansa. Shin ba su cancanci, saboda babansu, saboka kakansu ko saboda yan’uwantaka da  manzon All..(s) a jira, su kammala jana’izar manzon All..(a) ba, kafin a yi maganar magajinsa ba?.

Wanda kuma ya karanta Tarihi zai fahinci cewa daga ranar da manzon All..(s) ya bar duniya, iyalan gidansa masu tsarki suna cikin bakin ciki, da tsoro da wahala har yau da muke magana. Saboda musibar da al-ummar ta haddasa masu

Da zaran ya yi wafati aka yi watsi da zurriyarsa, banda haka sai suka maida su abokan gaba.

Wannan duk tare da ayoyin alkur’ani da hadisan manzon All..(s) wadanda suka yi meganar matsayinsu, na tsarki da ilmi da wajibcin sonsu, kan dukkan musulmi. Amma akasin abinda All..da manzonsa (s) suka yi umurni dangane da su ne, ya ke faruwa.

An ruwaito khalifa Umar ya ce duk wanda ya sake kira zuwa irin bai’ar da aka yiwa Abubakar, wato babu shawara to  a kashe shi.

Sannan a lokacinda zai mutu ya kafa kwamitin muta ne shida don su zabi daya daga cikinsu.

Amirulmuminina (a) yana daga cikin wadanda ya sanya a cikin wannan kwamitin kamar yadda zamu gani nan gaba.

Sannan shi ne Abdurrahman dan Auf shugaban kwamitin ya fara gabatarwa tayin Khalifancin tare da sharuddan ta. Wato hukunci da littafin All..da sunnar manzon All..(s) da kuma bin abinda shehunai biyu (Abubakar da Umar ) suka tafi a kai. Sai Imam ya ce masa ya amince da littafin All..da sunnnan manzon All..(s), amma ba zai bi sunnar Abubakar da Umar ba. Da haka kuma khalifanci ta kubuce masa a lokacin.

Da haka kuma aka zabi Khalifa Uthman, wanda ya amince da sharuddan, kuma bai yi amfani da su ba. Wanda ya kai ga kashe shi bayan shekaru 12 yana mulki.

Daga cikin wadanda suka ki yi yiwa Abubakar Bai’a akwai Amirulmuminin Aliyu dan Abitalib (s). Bayan ya kammal jana’izar Manzon All..(s).

Ya fi to daga daka gidan manzon All..ya koma gidansa ya zauna, sannan aka bashi labarin sauran abubuwan da suka faru bayan wafatin manzon All..(s).

Imam Ali (a) yaki bai’a wa Abubakar a lokacinda ya aiko masa ya zo yayi masa bai’a. Sannan ya yi fushi sosai da Abubakar da kuma wadanda suka amince suka yi masa bai’a.

Ya kuma hujjace su a duk tsawon rayuwarsa kan cewa Abubakar ya kwace hakkinsa. Ya ce bai yi tsammanin wani musulmi za iyi jur’a ya hau kan mimbarin manzon All..(s) a bayansa ba, don hakkinsa ne.

Sannan a lokacinda Abbas Ammin manzon All..(s) ya ga abin da ya faru, sai ya je wajen Aliyu (a) ya na cewa masa : Ya dan dan’uwa na ! ka shimfida hannunka in yi maka mubaya’a, mai yuwa mutane za su ce ammin manzon All..(s) ya yi bai’a ga dan ammin manzon All…(a)

Duk da cewa a cikin Banu Hashim a lokacin, babu wanda ya fi Abbas dan Abdulmuttalib shekaru, amma shi musuluncinsa, daga karshe-karshe rayuwar manzon All..(s) ne. Wato a shekara ta 8 bayan hijira. Wato a shekarar da manzon All..(s) ya kwace Makka. Har ana cewa, shi mutum  na karshe da yayi hijira Makka zuwa Madina. Saboda yana kan hanyar hijira ne sai ya hadu da manzon All..(s) ya na zuwa Makka, don kace shi daga hannun Mushrikai.

Banda shi sai Aliyu(s) wanda shi ne na farkon musulunta, kuma renon manzon All..(s) kuma mijin diyarsa tilo da ya bari a bayansa. ..

Dangane da wannan an ruwaito daga Ummu Aimanu, tana fadawa manzon All..(s), tana cewa (kana kiransa dan’wanka, amma kuma ka auram masa diyarka?). Kowa ya san cewa dan’uwansa ba wanda suka hada daya daga cikin iyaye ko biyu duka ba.

Banda haka, ga matsayinsa a cikin al-amuran musulmi tun farkonsa har zuwa karshe. Babu wani yakin da Aliyu (s) ya halatta, a duk yake yaken manzon All..(s) face shi ne gwazonsa.

Don haka babu shakka Aliyu (a) ya na da babban matsayin a cikin musulmi, wanda ba wanda ya isa ya yi inkarin hakan. Don haka ne, A lokacinda amminsa Abbas ya fadawa masa, ” Ka shinfida hannun ka, Ya kai dan dan’uwa na, in yi maka bai’a watakila mutane su ce: ammin manzon All..(s) ya yiwa dan’ammin manzon All..(s) bai’a, ba zasu yi sabani a tsakaninsu ba.

Sai Imam (a) ya ce masa, ya ammi, wa yake da’awar wannan matsayin ba mu ba?).

Ga shi manzon All..(s) ya dora masa Khalifin a gaban Jama’a a Ghadir Khom, kwanaki 70 kacal kafin wafatinsa, ta yaya wani zai ce bai sanda da haka ba?, hada da hadisan manzon All..(s) a wurare da dama, wadanda suke tabbatar da cewa Khalifanci na Ali (a) ne.

Dangane da wannan Taha Hussain wani  malamin tarihi a kasar masar ya na fada a cikin littafinsa mai suna ‘Ali wa Banuhu.’ …. Manzon All…(s)…ya fada masu: Matsayinka da ni, kamar matsayin Haruna da musa ne, sai dai ba bu annabi a baya na. Wata rana ya fadawa musulmi, duk wanda na kasashen shugabansa ne, to Aliyu shugabansa ne, da wasu hadisai da dama a kan hakkin Aliyu (a) na gadar manzon All..(s) a shugabancin al-ummarsa a bayansa.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

==========================================.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: wafatin manzon All iyalan gidan wadanda suka masu sauraro ya yi wafati duk wanda ya wa Abubakar Abubakar ya

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas: Za A Mika Gawawwakin ‘Yan Mamaya Da Kuma Fursunoni Rayayyu A Ranakun Alhamis Da Asabar

Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.

 A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na  gaba na musayar fursunoni.

 Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya za su saki sauran fursunonin da suke rike da su.

Shugaban na kungiyar Hamas ya bayyana hakan da cewa, yana nuni da yadda kungiyar take aiki da yarjejeniya, tare da yin kira da a tilasta HKI ta yi aiki da sharuddan yarjejeniyar ba tare da jan kafa ba. Haka nan kuma ya bayyana cewa kungiyar ta Hamas tana cikin shirin ko-ta –kwana na shiga shafi na gaba wanda shi ne dakatar da yaki da kuma janyewar sojojin mamayar daga Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
  • Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano
  • Hamas: Za A Mika Gawawwakin ‘Yan Mamaya Da Kuma Fursunoni Rayayyu A Ranakun Alhamis Da Asabar
  • Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane
  • Kissoshin Rayuwa. Sirar Imam Alhassan (a) 19
  • Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
  • Kasar Iran Zata Aika Da Tawaga Mai Karfi Zuwa Jana’izar Sayyid Nasarallah
  • Hamas Ta Sanar Da Shahadar Wani Jagoranta Da HKI Ta Kashe A Lebanon
  • Kasar Sin: Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba Wajen Kartar Kasashe Masu Karfin Iko Ba Ne
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Tituna Akan Kudi Naira Biliyan 6.3