Kasuwanci: Yadda matan Arewa ke samun arziki daga cikin gidajensu
Published: 15th, February 2025 GMT
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics).
Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta.
Labarin Salma na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan nan suke yawan samun muhawara a kafofin sada zumunta kan, wanda ya fi, tsakanin mallakar digiri da kuma ilimin sana’a.
A bangare guda kuma, mata da dama a yankin Arewa, musamman Jihar Kano, sun mayar da gidajensu, musamman ma kicin dinsu wata karamar masana’antar sarrafa kayan makulashe da abinci iri-iri, har suke samun shahara da ita. Zuwan kafofin sada zumunta kuma na kara saukaka samun kwastamomi daga ko’ina a fadin duniya, baya ga makudan kudaden da kafofin suke biyan masu wallafa bidiyoyi da hotunan a shafukansu, saboda tarin mabiyan da suke kara musu.
Kasuwancin mata a Arewa
Alkaluman da Bankin Mata na Duniya ya fitar sun nuna Nijeriya ce ke kan gaba a duniya wajen yawan matan da ke harkokin kasuwanci, wadanda adadin da ya kai miliyan 23. Kazaika kididdigar ta nuna kashi 41 na kananan sana’o’in kasar suna hannun mata ne. Rahoton ya ce bayan annobar Kwarona yawan mata da ke amfai da intanet musamman kafofin sada zumunta wajen fadada sana’o’insu ya karu zuwa kashi 67.9.
Tun zamanin kaka da kakakanni mata ke yin sana’o’i a Arewacin Nijeriya, musamman irinsu dinki da saka da kadin auduga, da suka shahara a matsayin sana’o’in mata.
Mata a Jihar Kano, cibiyar Arewa, sun kawo wani sauyi a tsarin sana’o’insu, inda daga cikin gidajensu suke bunkasawa tare da fadada harkokin nasu ta hanyar sayar da hajojinsu ta intanet da kuma manyan shagunan zamani.
Aminiya ta tattauna da wasu mata uku da ke kasuwanci daga gidajennsu — masu suna Salma Muhammad Salisu da A’isha Auwal da kuma Rukayya Nazir — amma suka sauya mata akala domin tafiya daidai da zamani.
Tafiya da zamani da kuma inganci
Salma ta ce, “Na halarci taruka da dama domin samun horo a harkar kasuwanci da tsara girki yadda zai ja hankalin kwastoma domin na samu kayana su samu gurbi a manyan shaguna.
“Sana’ata ita ce sayar da lemuka iri-iri na mutum daya ko taruka. Amma wanda na fi suna da shi shi ne lemon Mangwaro. Asali ni ba ni da sha’awar shan kayan marmari a yadda suke sai na markada. A nan ma na samu dabarar fara sana’ar tawa. Ina zuba lemon ne a robobi da kwalabe masu kyau da kaina, na rarraba a shaguna a sayar min.
“A shekarar 2020 na yi rajistar kamfanina da Hukumar Yi wa Kamfanoni Rajista (CAC), na kuma kara yawan nau’ikan lemukan da nake yi. Ina sayar da lemukan gargajiya irinsu sobo da tsamiya, sai kuma na zamani da nake yi domin taruka daban-daban sai wanda ka zaba,” in ji Salma.
Ta ci gaba da cewa, ba ta fara samun manyan kudi ba a sana’arta, sai da ta shiga wata kungiyar kwararrun mata masu sana’ar girki da ake kira ‘Chefs Dedterity Food Forum’. Daga nan ne ta samu damar fara sayar da kayanta a manya-manyan shaguna sayar da kayayyaki na Kano, da manyan gidajen abinci.
Wannan bayani na Salma ya yi daidai da alkaluman da Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO) ta fitar da ke nuna kashi 40 na masu kanana da matsakaitan masana’antu a Nijeriya mata ne, adadin da ya doke na sauran kasashen Saharar Afirka, wadanda ke da kaso 29 kacal.
Sana’ar gireba
Ita ma Aisha Auwal matshiya ce da sana’arta ta sayar da gireba ce, kuma soyayyarta da girki ta fara ne tun tana karama lokacin da take taya mahaifiyarta yin alkaki da dakuwa.
Ita ma kamar Salma, ta kammala digirinta na farko a shekarar 2016 a fannin Shari’a Addinin Musulunci. Ta jarabawa sana’o’i da dama kafin ta tsaya ga sayar da gireba, bayan ta gano wagegen gibin da ake da shi na kayan kwalam da makulashen Hausawa a Nijeriya. Daga nan ne ta yanke shawarar fara sayar da girebar ta hanyoyin zamani har ta fara samun muhalli a manyan shaguna a Kano.
A’isha ta ce, “Na fara ne a 2023 da N20,000 zuwa N40,000, a lokacin ina tallatawa a shafina na WhatsApp. Idan na saka aka saya, ni da maigidana sai mu kai wa mutum har gida. Hakan ya samar min kwastamomi sosai. Daga nan ne na ci gaba da tallata girebar a sauran shafuka kamar Instagram da Facebook. To, gaskiya a nan na samu tarin kwastamomi da har yanzu suna sayen kayana.”
Yadda na koyi tallata haja — Rukayya
Ita kuwa Rukayya Nazir mai shekaru 19 ta ce ta fara kasuwanci ne da sayar da tufafi a soshiyal midiya kafin ta koma sayar da ruwan sha a mazuban zamani. A cewarta, a nan ne ta samu karin ilimin kula da kwastoma da kuma dabarun tallata hajojinta.
Rukayya ta ce kasancewar, “Ina son girki, don haka da na fara tunanin mayar da shi sana’ata sai na shiga makarantar koyon sana’ar girki a Kano. A nan ne na koyi girke-girkenmu da dama na gida da na kasashen waje. Na fara ne da girkin abinci, kafin daga bisani na koma gasa kek da sauran kayan kwalam irinsa.”
A halin yanzu da sana’arta ta sarrafa kek iri-iri da sauran girke-girke Rukayya ta yi suna, musamman ga masu sayayya a manyan shaguna. Kek dinta ya fita daban ne a Kano, saboda sabon tsarin da ta bullo da shi na sanya kek din a karamin mazubin roba kuma take kiran sa ‘Cake-in-a-jar’.
Alfahari da magance kalubale
Rukayya ta ce kawo tsarin mazubin kek na roba da ta bullo da shi a Kano shi ne babbar nasarar da take alfahari da ita har zuwa yanzu.
Ta ce, “Da fari mutane sun ki karbar sabon tsarin saboda ba su saba da shi ba. Amma daga baya da suka dandana suka ji yadda yake, sai suka karba hannu bibiyu.”
Duk da wadannan nasarorin da matan suke samu, sun bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a sana’artata da kuma yadda ta shawo kansu.
A’isha Auwal ta ce kalubalenta na farko shi ne daina sayar da kayanta da shagon da ta fara kai wa gireba suka yi, ba tare da ba ta wani kwakkwaran dalili ba.
Ta ce, “Na tambayi Manajan ya ce babu komai matsaya ce kawai suka dauka a shagon.”
Ganin haka, domin magance matsalar, “Tun daga lokacin na daina kai wa shago daya kaya. Ina kaiwa wurare da yawa ta yadda ko da mutum daya ya ki sayar min, ba zai shafi kasuwancina ba sosai.
“Abu na biyu shi ne yadda wasu mutanen ba sa daukar sana’ar mata da muhimmanci. Gani suke kamar wasa ne musamman kasancewata matashiya. Sai kuma yanayin da tattalin arzikin Nijeriya ke shafar kayana. Misali, kowanne lokaci kayan hada gireba irinsu fulawa da sukari na iya samun karin farashi.
“To na kan zauna in yi lissafin yadda za a yi na ci gaba da yin girebar ba tare da na rage ingancinta daga yadda nake yi ba. Don haka sai da ni ma na kara farashi. To kuma dole sai na duba yadda za a yi karin nawa ba zai korar min kwastamomi ba. Idan kuma na rage farashin da yawa ba, lallai na iya ci gaba da sana’ar ba.
“Don haka dole kullum cikin lissafin yadda zan kara kudi kadan ba tare da sana’ar ta gurgunce ba nake. Sai kuma ita kanta girebar. A lokutan damina ba na yin ta sosai saboda danshi yana shafar dadewarta. Amma dai ina kara fadada bincike kan dabarun zamani da yadda za a inganta ta a irin wannan lokacin.”
Satar fasaha da rashin lambar NAFDAC
A nata bangaren Salma ta ce ta ce samun lambar Hukumar Kula da Ingancin Abinci ta Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ce babbar matsalar da ta sako ta a gaba, domin har yanzu ta gaza samu.
“Wannan yana shafar sana’ata saboda wasu shagunan ba sa karbar kayan da ba su da lambar. Amma da zan samu, zan wuce matsayin da nake a yanzu. Sai kuma wata matsalar ita ce wasu shagunan da sun fara karbar lemon suna sayar min, sai su daina. Sai kuma su fara kwafar nawan suna sayarwa.”
Rukayya Nazir a nata bangaren, kalubalen da ta farko cin karo da shi, shi ne na kin karbar salon ‘Cake-in-a-jar’ ne da mutane suka yi. Amma daga baya da ta yi amfani da soshiyal midiya da kuma rabon kek din kyauta, sai ta shawo kan lamarin.
Bukatar cin moriyar tallafin sana’o’i
Labarin wadanann mata abin sha’awa ne, musamman a wannan lokacin da aikin gwamnati ya yi karanci, ake kuma fama da matsalolin tattalin arziki. Sai dai nasarar kowacce sana’a na da alaka da samun ilimin gudanar da ita da kuma jari, abin da ya yi karanci sosai sosai a hannun mata musamman a Arewacin Nijeriya.
Duk da cewa Gwamnatin Tarayya na da shirye-shiryen tallafa wa matsakaita da kananan sana’o’i irinsu GEEP da kuma WinBiz na mata masu sana’o’i, matan Arewa da dama, musamman na kasa-kasa ba sa amfana da su. Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da rashin sanin yadda za su ci gajiyar wadannan tsare-tsare ba.
A bangaren samun tallafin da ba na gwamnati ba ma, an bar matan Arewa a baya. Shirye-shiryen kungiyoyi irinsu ‘She Leads Africa’ da na gidauniyar ‘Tony Elumelu’ da ke bayar da horo da kudaden tallafi, na wuce su, saboda karancin wayar da kai kan hanyoyin cin gajiyar shirye-shiryen.
Don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki su zage dantse domin wayar da kan al’umma kan irin wadannan tsare-tsaren da ke samar da ci-gaba ga jihohin da ma kasa baki daya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kasuwa Kasuwanci a manyan shaguna
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Gudanar Da Tantance Sabbin Kwamishinoni
Kakakin Majalisan ya amince da kudirin dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana kuma shugaban Kwamitin Majalisar kan Muhalli, Hon. Muhammed Adamu Omadefu, wanda ya bukaci dakatarwar a yayin tantance kwamishinan a zauren Majalisar da ke Lafiya, babban birnin jihar.
Hon. Jatau ya ce, Majalisar za ta sake duba batun tantance shi ne kawai idan ya aika da wasikar neman uzuri mai karfi ga Majalisar kan aikata laifi da rashin biyayya da ya yi lokacin da yake Kwamishina.
Ya ce, Majalisar ba za ta bari wani jami’in gwamnati ya zubar da darajar Majalisar ba.