Mummunan Hatsari Ya Kashe Mutane 23, Da Yawa Sun Jikkata A Kano
Published: 15th, February 2025 GMT
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin da ya afku a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a ranar Juma’a nan da ta gabata.
A cewar hukumar FRSC, hatsarin ya rutsa da wata tirela ce wacce take ɗauke da kayayyaki da fasinjoji.
Binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci wanda aka fi alakƙanta shi da faruwar lamarin. Hatsarin ya rutsa da a ƙalla mutane 71, inda 48 suka samu raunuka, yayin da 23 suka mutu.
Jami’an bayar da agajin gaggawa na FRSC tare da haɗin gwuiwa da rundunar ‘yansandan Nijeriya sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano
Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida.
Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar.
Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan TsaroA cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi.
Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa.
Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin, inda suka bayyana cewa gobarar ta lalata gidaje guda shida, kaya, hatsi, dabbobi da kuma wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne sakamakon wuta da aka yi amfani da ita wajen dafa abinci, amma aka bar ta ba tare da an kashe ba.
Sarkin ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa kuma ya ba su tallafin Naira 200,000 domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.