Sojojin HKI Sun Kashe Falasdinawa 4 A Safiyar Yau Asabar A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Published: 15th, February 2025 GMT
Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin yahudawan sun kashe Adel Abdel Bashkar a sansanin yan gudun hijira na Askar a kusa da garin Nablus bayan albarusai sun sameshi a kirjinsa.
Labarin ya kara da cewa bayan an kai shi asbine sai yace ga garinku, ko kuma yayi shahada.
Har’ila yau majiyar ta kara da cewa Falasdinawa matasa uku ne suka yi shahada a lokacinda sojojin yahudawan suka kai hari a sansanin yan gudun hijira na Nurusham.wanda yake kilomita 1.8 daga garin Tulkaram .
Wadanda suka yi shahadar sun hada da Jihad Mahmoud Hassan Masharqa, dan shekara 40, a duniya. Muhammad Ghassan Abu Abed, dan shekara 23 a duniya sai kuma Khaled Mustafa Sharif Amer, sannan labarin nya ce yahudawan suna rike da gawakinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Fara Ficewa Daga Wasu Wurare A Kudancin Kasar Lebanon
Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai kyautata al-amuran tsaro a yankin. Wanda kuma zai tabbatar da ikon kasar Lebanon a kan dukkan kasar ta.
Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Lebanon ta bokaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar. Sannan bisa kudurin mai lamba 1701 na MDD rundunar UNIFIL zata taimaka wa sojojin kasar tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin HKI da kuma kasar Lebanon.
Labarin ya kara da cewa an ga sojojin Lebanon suna shiga yankunan da sojojin HKI suke ficewa a safiyar yau.
Sojojin lebanon sun shiga Maroun El Ras, Mahbib, Meiss Jabal, Blida, Houla da kuma Markaba.