Kasashen Larabawa A MDD Sun Yi Watsi Da Shirin Trump Na Korar Falasdinwa Daga Gaza
Published: 15th, February 2025 GMT
Jakadun kasashen larabawa da kuma na wasu kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa daga yankin Zirin gaza, saun kuma bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Shirin Trump na korar Falasdinawa daga Gaza dai ya fusata kasashen duniya musamman kasashen larabawa da musulmi, sun kuma ki amincewa da duk wani abu da zai sauyawa Falasdinawa kasarsu.
Wannan yana faruwa ne bayan da HKI ta kasa kwace zirin Gazar a hannun mayakan Hamas da kawayenta na wasu kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin.
Amurka tana son abinda yahudawan basu same shi a yaki ba Trump ya zo ya kwace shi ya mika masu ba tare da wata wahala ba. Sun ki amincewa da hakanne don ya sabawa doka ta 49 na MDD ta shekara 1949, inji Al-Bannai wanda yake magana a madadin kasashen laraba.
Kungiyar kasashen larabawa dai sun ki amincewa da hakan sun kuma sami cikekken goyon bayan kungiyar OIC ta kasashen musulmi da kuma kungiyar yan ba ruwammu, wato ‘the Non-Aligned Movement’ (NAM).উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.