Hare-Haren Isra’ila Sun Keta Yarjiyar Tsagaita Wuta A Kudancin Kasar Lebanon
Published: 15th, February 2025 GMT
Jiragen Yakin HKI Sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a kudancin kasar Lebanon, wanda hakan keta yarjeniyar tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu.
Kamafanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kusa da kogin Litan, Yohmor Al-shaqif da kuma Zoutr Al-sharqiyya, da kuma Deir Siryan, zibqin da Yater.
Gwamnatin HKI ta bayyana cewa ta kai hari ne kan rumbunann ajiyar makamai na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.
Duk ntare da tsagaita wuta tsakanin Hizbullah da kuma HKI a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, bayan watanni 14 da fafatawa, sojojin HKI sun ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar Lebanin suna kashesu suna lalata makamasu suna kuma rurrusa gidajensu.
Gwamnatin kasar Lebanon ta shigar da kara a gaban MDD kan kan keta hurumin da HKI yiwa yarjeniyar tsagaita wuta a kasar ta Lebanon amma babu wani abu da ta iya in banda yin allawadai da shi. A ranar 27 ga watan Jenerun da ya gabata, gwamnatin kasar Lebanon ta amince ta tsawaita kasancewar sojojin HKI a kudancin kasar Lebanon.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma wannan yanki shi ne tushen al’amuran duniya da dama, to amma a baya-bayan nan ya fara ne da harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsah wanda kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tsara ta kuma aiwatar da shi, wanda ya zama babbar nasara a kan ‘yan sahayoniya, wannan lamari ne mai muhimmanci.