Zaɓen Katsina: An Samu Ƙarancin Masu Kaɗa Ƙuri’a Da Zargin Sayen Ƙuri’u
Published: 15th, February 2025 GMT
Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, inda ake fuskantar ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma zargin sayen ƙuri’u a wasu rumfunan zabe.
Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da NSCDC, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga tare da tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro.
A rumfar Birchi ta Kudu, inda aka yi rajistar masu zabe 808, kaɗan daga cikinsu ne suka bayyana, wasu kuma sun ce an basu ₦500 bayan sun kaɗa ƙuri’unsu. Duk da babu rahoton tashin hankali, ƙarancin fitowar masu zaɓe da zargin sayen ƙuri’u na ƙara haifar da shakku kan ingancin zaɓen.
কীওয়ার্ড: Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin: Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba Wajen Kartar Kasashe Masu Karfin Iko Ba Ne
A ranar 15 ga watan Fabrairu, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun yi shawarwari a Munich na kasar Jamus. A cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, a karon farko, sun bayyana goyon bayansu ga yadda Taiwan za ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka dace, tare da jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun, ya sake nanata cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi da ita ba, kuma batun Taiwan lamari ne na cikin gidan kasar Sin kawai, kuma ba ta yarda da wata tsangwama daga waje ba. Shigar Taiwan cikin ayyukan kungiyoyin kasa da kasa dole ya kasance bisa ka’idar Sin daya tak a duniya. A ko da yaushe kasar Sin tana adawa da yadda wasu kasashe ke hada kai wajen kafa kananan kungiyoyi, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin, tare da suka da bata wa kasar Sin suna, da tayar da husuma da adawa, kana ta mika wa kasashen da abin ya shafa gamsasshen korafi.
Bugu da kari, a matsayin martani ga kwaskwarimar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kan takardar sahihancin bayanai kan dangantakar Amurka da Taiwan, Guo Jia Kun ya bukaci bangaren Amurka da ya gaggauta gyara kuskuren, da kuma mutunta ka’idar Sin daya tak da sanarwoyi guda uku na Sin da Amurka, kuma ta bi a hankali wajen tinkarar batun Taiwan. (Mohammed Yahaya)