Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama.

Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin hanci a lokacin, sai aka buɗe bincike nan take, ko da yake babu wanda ya shigar da ƙorafi kai-tsaye.

Ya bayyana cewa, ziyarar Gambaryan ta biyu ta kasance wani ɓangare na bincike kan yadda ake amfani da kamfanin hada-hadar kuɗi na Binance don sarrafa darajar naira.

Ya ce, amma binciken ya gamu da cikas sakamakon dabarun da Gambaryan da tawagar sa suka yi amfani da su.

Ministan ya ƙara da cewa, Gambaryan ya samu ‘yanci a watan Oktoba na 2024 bisa dalilai na jinƙai, bayan cimma matsaya tsakanin Nijeriya da Amurka da ta kawo fa’ida ga Nijeriya.

Ya kuma ce gwamnati ta yi watsi da tayin da Binance ya yi na biyan dala miliyan 5 domin a saki Gambaryan, inda ta amince da wata yarjejeniya mai amfani da gwamnatin Amurka.

“Muna ƙaryata duk wata magana da Mista Gambaryan ke yi kan jami’an gwamnati da ke da hannu a shari’ar sa, kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan ƙarairayi baki ɗaya,” inji Idris.

Ministan ya bayyana cewa zargin da Gambaryan ke yi babu hujja, kuma bai da inganci duba da cewa yana ƙoƙarin ɓata suna da razana waɗanda suka tabbatar an gurfanar da shi a gaban shari’a ne.

Ministan ya ce yana da yaƙinin cewa, tsarin shari’a na Nijeriya da na Amurka za su ba Gambaryan damar gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi.

A halin yanzu, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi hankali kada su faɗa tarkon waɗannan ƙarairayi da ƙazafi da wannan Ba’amurken yake yaɗawa.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Edwin Clark

 

Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.

 

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

 

Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.

 

Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci gaban Najeriya.

 

“Fafutukarsa da hikimarsa da jajircewarsa wajen ci gaban kasa sun sa, ya zama murya mai matukar tasiri a siyasar Najeriya,” in ji Minista.

 

“Za a yi matukar rashin shawarwarinsa masu hikima da gudunmawarsa wajen gina kasa.”

 

“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Cif Clark, gwamnatin da al’ummar Jihar Delta, da dukkan ‘yan Najeriya da suka amfana da rayuwarsa mai albarka. Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalansa da duk masu jimamin wannan rashi babban hakuri da karfin zuciya.”

 

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
  • Zargin Daukar Nauyin Boko Haram: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Akpabio A Villa
  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Dattijon Kasa, Edwin Clark
  • USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Edwin Clark
  • Shugaban Amurka Ya Ce: Sun Baiwa Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Damar Ya Aikata Abin Da Yake So
  • Hauhawar farashi ya koma kashi 24 a Nijeriya — NBS
  • Gwamnati Ta Buƙaci Sauƙaƙa Tsarin Samar Da Biza Don ƙarfafa Kasuwancin ‘Yan Nijeriya A Duniya
  • Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Daga Riƙe Wa Ƙananun Hukumomin Kano 44 Kuɗaɗensu