Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto
Published: 15th, February 2025 GMT
Wani ɗan Nijeriya ɗan asalin Jihar Yobe, Saidu Abdulrahman, ya lashe kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya a matsayin wanda ɗaukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya.
Bayanai sun ce a cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali a watan Satumba na bara, lamarin da ba shi damar doke wanda ya lashe kambun na bara da hotuna 500.
Da wannan ƙwazo ne Kundin Bajinta na Duniya wata Guinness World Records (GWR) ya karrama matashin da lambar yabo.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, matashin ya bayyana cewa, “ina mai farin cikin sanar da cewa, an karrama ni a hukumance da matsayin mai riƙe da kambun tarihi na Guinness saboda na mafi ɗaukan hotunan da yawa waɗanda na ɗauka cikin sa’a ɗaya!
“Karɓar shaidar lashe lambar yabo ta kudin Guinness World Records, sakamako ne na jajircewa ta da kuma goyon baya mara iyaka daga dangina da abokaina, da jagororina, da masu yi min fatan alkhairi waɗanda suka kasance tare da ni.”
Ya ce “Nasarar kafa wannan tarihi na ɗaukar hotuna 897 a cikin minti 60 kacal, ba tawa ce ni kaɗai ba; ta duk ɗan Nijeriya ce da ya amince da ni, ya taimaka min, ya kuma jinjina min tun daga lokacin da na fara har gama.”
“Kafa wannan tarihi shaida ce ta cewa za mu iya yin bajinta a duniya.”
Haka ita ma cikin wani saƙo da Kundin Bajintar ya wallafa, ya ce “Abdulrahaman ya yi yunƙurin kafa tarihin ne domin wayar da kan jama’a game da ɗaukar hoto a Nijeriya.
TRT dai ya ruwaito cewa an ba shi lambar yabon ce a garin Potiskum da ke Jihar Yobe, kana taron ya samun halartar jami’an gwamnatin jihar da ɗalibai da kuma masoyansa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kundin Bajinta na Duniya Sa idu Abdulrahman Kundin Bajinta na Duniya lambar yabo
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp